Cikakken jerin Gwamnonin Katsina tun daga kirkirar Jihar
A yayin da Jihar Katsina ta cika shekaru 30 da kafuwa a Najeriya mun kawo maku jerin Gwamnonin Jihar tun daga shekarar 1987 kawo yanzu.
1. Kanal Abdullahi Sarki Mukhtar
Kanal Sarki Mukhtar shi ne Gwamnan farko kuma Soji da ya mulki Jihar daga Satumban 1987 zuwa Agustan 1988.
2. Kanal Lawrence Onojo
Onoja yayi mulki daga lokacin da Kanal Mukhtar ya sauka da watanni biyu zuwa karshen shekarar 1988.
3. Kanal Yahaya Madaki
Yahaya John Madawaki ya karbi ragamar mulkin bayan Onojo har zuwa shekarar 1992 lokacin da aka yi zaben siyasa.
4. Saidu Barda
Alhaji Saidu Barda ya lashe zaben Gwamna na farko a Jihar a karkashin Jam'iyyar NRC kafin a sauke Gwamnonin.
KU KARANTA: Za a shiga wani mugun yajin aiki a Jihar Kogi
5. Kyaftin E.A Acholonu
Acholonu wanda shi ma Soja ne ya karbi mulkin Jihar a lokacin Shugaba Janar Abacha bayan an sauke Gwamnoni farar hula.
6. Kanal Samaila Bature
Kanal Chama yayi mulkin sa ne daga tsakiyar 1996 bayan Acholonu har zuwa tsakiyar shekarar 1998.
7. Laftana Kanal Joseph L. Akaageger
Akaagegar yayi mulkin sa na kusan shekara guda daga 1998 zuwa 1999 lokacin da aka dawo farar hula.
8. Alhaji Umaru Yaradua
Tsohon Shugaba Ummaru Musa Yaradua ya lashe zaben 1999 a karkashin PDP inda yayi shekara 8 daga nan ya zama Shugaban kasa.
9. Ibrahim Shehu Shema
Bayan Marigayi Yaradua sai Barista Ibrahim Shema wanda shi ma tayi shekaru 8 kan karaga zuwa 2015.
10. Rt. Hon. Aminu Masari
A shekarar 2015 ne Aminu Bello Masari ya dare kujerar Gwamna a karkashin Jam'iyyar adawa ta APC.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Mahaifin Jagoran Biyafara Nnamdi Kanu yana jawabi
Asali: Legit.ng