Tuna Baya: Lokacin da Jonathan Ya Fusata Amurka da Sa Hannu a Dokar Hana Auren Jinsi
- A lokacin yana shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan ya amince da dokar haramta dangantakar jinsi a Najeriya
- Shugaban Najeriyan ya jawo fushin kasashen yamma masu goyon bayan LGBT a dalilin wannan mataki da ya dauka
- Gwamnatin Goodluck Jonathan ta yaki auren jinsi da kafa kungiyoyi ko gidajen da ake luwadi ko madigo a kasar nan
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - A wata ranar 13 ga watan Junairu 2014, Dr. Goodluck Jonathan ya sa hannu a dokar da ta jawo maganganu iri-iri.
Shugaban Najeriya a lokacin, Dr. Goodluck Jonathan ya amince da kudirin da ta haramta aure da duk wata dangantakar jinsi.
The Guardian ta rahoto cewa Mai girma Goodluck Jonathan ya kawo dokar da ta laftawa luwadi da madigo daurin shekaru har 14.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dokar haramta alakar jinsi a Najeriya
Duk wanda aka samu ya auri jinsinsa ko dai wata alaka zai iya shafe shekaru 14 a daure.
Dokar ta haramta rajista ko kafa gidajen luwadi ko madigo ko kuwa a kirkiro wata kungiya da ke goyon bayan muradun LGBT.
Wanda aka samu ya na tallata wannan danyen aiki ko ya fito fili yana nuna alakarsa da jinsisa a fili, zai iya yin shekaru 10 a daure.
Auren jinsi: Amurka ta kalubalanci Jonathan
Sakataren gwamnatin Amurka, Mista John Kerry ya yi tir da dokar, ya nuna ba su goyon bayan matakin da Dr. Jonathan ya dauka.
Baya ga haramta aure ko wata alaka tsakanin maza ko mata, gwamnatin Barrack Obama ta ce wannan doka ta take hakkin Bil Adama.
A lokacin, an ji John Kerry ya yi ikirarin jama’a suna da hakkin sha’awar abin da suke so, sai dai auren jinsi bai iya samun karbuwa ba.
Shekara da shekaru ana yakar auren jinsi
Reuters ta ce tun shekarar 2006 ake wannan yunkuri amma ba a iya cin ma nasara ba.
Mai girma Goodluck Jonathan ya rattaba hannu a kudirin, hakan yana nufin duk wanda aka samu da laifi zai shiga magarkama a Najeriya.
Za a duba auren jinsi a Samoa
Ana da rahoto cewa Majalisar kolin shari’ar addinin musulunci za ta bibiyi yarjejeniyar Samoa da gwamnati ta rattabawa hannu kwanan nan.
Sheikh Bashir Aliyu Umar ya tabbatar da cewa sai sun yi nazarin Samoa sannan za su dauki matsaya yayin da ake ta tir da matakin kasar.
Asali: Legit.ng