Barack Obama da Musulunci: Abubuwa 10 da baka sani ba

Barack Obama da Musulunci: Abubuwa 10 da baka sani ba

- Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama shine bakin mutum na farko da ya taba mulkin kasar Amurka

- Mutanen kasar Amurka sunyi murna da hawansa mulki duk da cewa ana cewa musulmi ne, amma dai babu cikakken bayane game da addininsa

- Amma dai Obama ba musulmi bane kuma ba kirista bane

Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama shine bakin mutum na farko da ya taba mulkin kasar Amurka.

Mutanen kasar Amurka sunyi murna da hawansa mulki duk da cewa ana cewa musulmi ne, amma dai babu cikakken bayane game da addininsa. Amma dai Obama ba musulmi bane kuma ba kirista bane.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram sun bunkasa ne saboda gwamnatin tarayya tayi bacci – Shehun Bama

1. Obama dai ba musulmi bane, kuma ba kirista bane. Ya mayar da hankalinsa akan aikinsa ne kawai, da al’amuransa na siyasa, kuma yana kokarin farantawa mutanensa rai.

2. Kakarsa musulma ce, kuma taje masallacin Haram don gabatar da Umrah a ranar 24 ga watan Afirilu shekarar 2015.

3. Obama ya bayyana cewa ya girma a gidan musulunci, kuma zauna a kasar musulunci ta Indonesia.

4. Mijin mahaifiyarsa na yanzu musulmi ne

5. Babansa na asali ma musulmi ne, dan kasar Kenya, kuma lokacin yarintarsa yana jin kiran sallah, duk da cewa bai karbi addinin musuluncin gaba day aba.

6. Channels, sun bayyana abubuwa dayawa da Obama yake yiwa garuruwan musulmi a kasar Turkiyya da sauransu.

7. Ya ziyarci kasashen musulunci da dama a lokacin da yake shugaban kasar Amurka, kuma yayi kokarin kawo karshen matsalar bambancin fata da kuma kabilanci cikin gaggawa.

8. Daya daga cikin muhimman abubuwan da suka sanya nake kara girmama shi, shine a koda yaushe yanaso musulmai su kasance a kujerun gaba idan zai koyar da dalibai a jami’ar Cairo dake kasar Egypt.

9. Babban abun mamaki shine a kowane azumi Obama yana shiryawa shuwagabannin musulunci abun buda baki.

10. A lokacin da ya kai ziyara kasar Turkiyya Obama ya bayyana cewa kasar Amurka ba kasar Kirista bace, kasace wadda mutanen kabilu daban-daban da addinai daban-daban.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng