CNG: Wahalar Fetur Za Ta Ragu, NNPC Ya Kaddamar da Gidajen Gas 12 a Abuja da Legas
- A yayin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke kokarin rage dogaro da man fetur, kamfanin NNPC ya bude gidajen man CNG 12
- An ruwaito cewa ministan albarkatun man fetur (Gas), Ekperikpe Ekpo ne ya kaddamar da gidajen man a Abuja da kuma Legas
- A cewar ministan, bude gidajen man CNG zai taimaka wajen rage sauyin yanagi, dogaro da man fetur da kuma bunkasa tattali
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya kaddamar da wasu gidajen sayar da gas din CNG guda 12 a Legas da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Ekperikpe Ekpo, karamin ministan albarkatun man fetur (Gas) ne ya kaddamar da sababbin gidajen man CNG a lokaci daya a ranar Alhamis.
Kamfanin NNPC ya bude gidajen CNG 12
Kamfanin NNPC ne ya fitar da sanarwar hakan a shafinsa na X inda ya bayyana cewa gas din CNG ya fi tsafta, kuma yana da saukin farashi yayin da zai kawo sauki ga 'yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a wajen taron, Ekperikpe Ekpo ya ce kaddamar da gidajen man zai bunkasa tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi ga 'yan kasar.
Ya kuma ce hakan zai ba da gudummawa sosai ga burin Najeriya na rage fitar da gurbattaccen hayaki, rage dogara da fetur da kuma yaki da sauyin yanayi.
NNPC zai gina gidajen LNG
Ministan ya yabawa kamfanin na NNPC bisa tabbatar da cewa man CNG ya samu ga ‘yan Najeriya, in ji rahoton jaridar The Cable.
A nasa bangaren, Mele Kyari, shugaban kamfanin NNPC, ya ce baya ga tura tashoshin CNG a fadin kasar, kamfanin da abokan huldarsa za su gina gidajen man gas din LNG guda uku.
Shi ma da yake nasa jawabi, wani manajan NNPC, Huub Stokman yace nan da shekara guda kamfanin zai bude gidajen man CNG sama da 100.
NIPCO ya gina gidajen man CNG 4
A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin iskar Gas na NIPCO ya ce ya kammala aikin gina gidajen sayar da iskar gas din CNG guda hudu a Legas.
Kamfanin NIPCO ya bada tabbacin dorewar samar da iskar gas da kuma siyar da shi a kan N200/ scm maimakon N670/L da ake siyan man fetur a Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng