Da duminsa: DPR ta janye bada lasisi ga gidajen man dake kusa da iyakokin Najeriya

Da duminsa: DPR ta janye bada lasisi ga gidajen man dake kusa da iyakokin Najeriya

Ma'aikatar lura da arzikin man fetur wato DPR ta daina bada daman gina gida mai tare da janye bada lasisi ga gidajen mai dake da kusancin kilomita 20 da iyakokin Najeriya har lokacin da Allah yaso.

Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa hukumar ta alanta hakan ga masu bukatar gina sabbin gidajen mai a yankunan.

DPR ta bayyana cewa dalilin da yasa ta yanke wannan shawara shine taimakawa muradun gwamnati na hana fasa kwabrin man fetur a iyakokin kasar.

Kakakin hukumar DPR, Paul Osu, ya ce: "Bisa ga wannan sanarwa, muna baiwa dukkan wuraren ajiye man fetur da yan kasuwan mai shawaran su daina kaiman fetur wuraren har sai sun sake tuntubarsu."

Wannan ya biyo bayan umurnin hukumar hana fasa kwabri wato Kwastam, inda ta hana sayarwa gidajen mai dake kimanin kilomita 20 da iyakokin Najeriya man fetur.

KU KARANTA: Motar Soji ta hallaka mutane 2 cikin Keke Napep, 3 sun jikkata

Mun kawo muku jerin garuruwan dake kusa da iyakokin Najeriya uku da wannan abin zai shafa:

1. Gamboru Ngala - Jihar Borno

2. Mubi - Jihar Adamawa

3. Garin-gada, Yunusari LGA

4. Maigatari - Jihar Jigawa

5. Daura - Jihar Katsina

6. Jibiya - Jihar Katsina

7. Illela - Jihar Sokoto

8. Ilo, Tsamiya, Bagugu - Jihar Kebbi

9. Kamba - Jihar Kebbi

10. Idiroko - Jihar Ogun

11. Seme - Jihar Legas

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel