Kotu Ta Umarci Alkalan da Abba Ya Nada Su Ajiye Kujerar Kwamitin Bincike Ganduje

Kotu Ta Umarci Alkalan da Abba Ya Nada Su Ajiye Kujerar Kwamitin Bincike Ganduje

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ya umarci alkalai biyu da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya ba wa mukami su ajiye aikin
  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta nada Masu shari'a Faruk Adamu da Zuwaira Yusuf shugabannin kwamitin binciken Abdullahi Ganduje
  • Gwamnatin Kano na binciken tsohon gwamna Ganduje da iyalinsa da laifin sama da fadi da kudin jama'ar lokacin ya na shugabantar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta umarci alkalan Kano guda biyu da su ajiye mukaman da gwamnatin Kano ta ba su na bincikar tsohon gwamna Abdullahi Ganduje.

Kara karanta wannan

Abba zai kammala muhimman ayyukan da Kwankwaso ya fara, Ganduje ya yi biris da su

Mai shari'a Simon Ambode ya umarci Mai Shari'a Faruk Adamu da Mai Shari'a Zuwaira Yusuf na babbar kotun Kano da su ajiye shugabancin kwamitin binciken almundahanar kudin jama'a da rikicin siyasa da yaran da su ka bata.

Jihar Kano
Kotu ta umarci alkalan Kano 2 su ajiye mukamin da Abba Kabir Yusuf da nada su Hoto: Ganduje TV/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Alkali Simon Ambode ya ba wa alkalan biyu awanni 24 su ajiye mukamin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya yi nasara a kotu

Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shigar da kara ya na tuhumar zaman Faruk Adamu da Zuwaira Yusuf daga shugabantar kwamitin da ke bincikensa, Vanguard ta wallafa.

A hukuncin da Mai Shari'a Amobeda ya yanke yau Alhamis, ya umarci hukumar kula da harkokin shari'a ta kasa (NJC) ta dakata da ba wa alkalan alawus alawus da sauran hakkokinsu idan su ka bijirewa umarnin.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gurfana a kotun Kano saboda zargin satar N322m a fashi da makami

Wannan na nufin tsohon gwamna Abdullahi Umar Gamduje ya yi nasara a shari'ar da ya shigar kan bincikensa da gwamnatin Kano ke yi.

An sauya kotun shari'ar Ganduje

A wani labarin kun ji cewa babbar mai shari'a a jihar Kano, Dije Abdu Aboki ta bayyana sauya kotun da ke sauraron shari'ar Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf na zargin tsohon gwamnan da wasu daga cikin iyalansa da almubazzarancin kudin mutanen Kano a zamanin gwamnatinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.