Hukumar JAMB Ta Bankado Mutane 3, 000 Masu Karyar Digiri da Takardun Karatu

Hukumar JAMB Ta Bankado Mutane 3, 000 Masu Karyar Digiri da Takardun Karatu

  • Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB ta bayyana gano wasu masu karyar kammala manyan makarantu a Najeriya
  • Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oleyede da ya bayyana haka ya kara da cewa matasa 3000 na rike da shaidar kammala makarantun
  • Haka kuma Farfesa Oleyede ya bayyana an gano wasu manyan makarantu masu bayar da damar karatu ga dalibai ba bisa ka'idar JAMB ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta bayyana cewa ta gano dubannan matasan kasar nan da ke karyar sun kammala manyan makarantu.

Akalla masu karyar kammala makarantun gaba da sakandare 3,000 hukumar JAMB ta ce ta bankado, wanda ta ke ganin hakan ya zama abin kunya.

Kara karanta wannan

"Dalibai 300,000 ake sa ran za su memi lamunin karatu" Inji NELFund

Karatu
JAMB ta gano masu karyar kammala jami'a 3000 a Najeriya Hoto: Emmanuel Arewa
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa ta gano yadda wasu manyan makarantun kasar nan ke daukar dalibai ba ya hanyar da ta dace ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dalibai 3000 na da shaidar bogi," JAMB

Shugaban hukumar shirya jarrabawar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana damuwa kan yadda wasu dalibai 3000 a kasar nan su ka yi karyar kammala jami'a.

Channels Television ta wallafa cewa shugaban hukumar ya ce da yawa daga dalibai ba su taba shiga aji ba, kuma yanzu haka su na rike da shaidar kammala karatu.

A gefe guda kuma ya ce abin kunya ne yadda wasu manyan makarantun kasar nan ke bayar da damar karatu ga dalibai da barauniyar hanya.

Ya ce hakan da su ke yi bai dace ba, ganin muhimmancin ilimi a kasar nan, kuma dama batun daukar dalibai ba bisa ka'ida na daga abubuwan da ke ci wa hukumar tuwo a kwarya.

Kara karanta wannan

Kano: KEDCO ya yanke wutar lantarkin jami'ar Dangote saboda taurin bashi

Mahaifi ya rubutawa dansa JAMB

A baya mun ruwaito cewa wani mahaifi ya shiga hannun hukuma bayan an gano shi ya zauna ya na rubutawa dansa jarrabawar JAMB, lamarin da ya saba doka.

Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce yanzu akwai kayan aikin da za su gano masu sojan gona.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.