An Yi Musayar Wuta Tsakanin Jami'an Tsaro da ’Yan Bindiga a Abuja, an Kubutar da Rayuka

An Yi Musayar Wuta Tsakanin Jami'an Tsaro da ’Yan Bindiga a Abuja, an Kubutar da Rayuka

  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai farmaki kauyen Guto da ke karamar hukumar Bwari, birnin tarayya Abuja
  • Rundunar 'yan sandan Abuja ta ce 'yan bindigar sun yi yunkurin yin garkuwa da wasu kananan yara mata guda biyu
  • Bayan dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaro da masu garkuwa da mutanen, an ce an kubutar da kananan yaran tare da mayar da su gida

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ce ta jami'an tsaro sun yi nasarar kubutar da kananan yara biyu da aka yi yunkurin garkuwa da su.

An ruwaito cewa wasu gungun 'yan bindiga ne suka farmaki kauyen Guto da ke karamar hukumar Bwari a ranar Lahadi, kuma suka sace kananan yaran.

Kara karanta wannan

Matar aure ta tsere daga hannun 'yan bindiga yayin da bacci yayi awon gaba da miyagun

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan harin 'yan bindiga a Abuja
Jami'an tsaro sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Abuja. Hoto: @FCT_PoliceNG
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun kai hari Abuja

Wata sanarwa da kakakin rundunar, Josephine Adeh ta fitar kuma aka wallafa a shafin rundunar na X ta ce kananan yaran biyu da aka yi garkuwa su mata ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Josephine Adeh ta kara da cewa 'yan bindigar sun sace yaran da misalin karfe 1 na rana inda suka tafi da su zuwa wani waje da ke kusa da jihar Neja.

Kakakin rundunar ta bayyana cewa sashen rundunar na yaki da masu garkuwa da mutane sun dura garin Guto tare da bin bayan 'yan bindigar.

'Yan sanda sun kubutar da kananan yara 2

Sanarwar ta ce:

"Dakarun hadin guiwa na 'yan sanda, mafarauta da DSS sun bi bayan 'yan bindigar, kuma sun yi masu kwantan bauna a dajin Gauraka da ke makotaka da Abuja.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji yan bindiga a Sokoto, sun ceto mutanen da suka kama

"An yi musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindigar, wanda ya tilastawa 'yan ta'addan tserewa tare da barin kananan yaran da suka yi yunkurin tafiya da su.
"A yayin da aka mika kananan yaran ga iyayensu, kwamishinan 'yan sandan Abuja, CP Benneth C. Igweh, na jaddada himmatuwar rundunar na wanzar da tabbatar da tsaro."

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki ofishin rundunar 'yan sandan Ishieke da ke jihar Ebonyi.

An ruwaito cewa 'yan bindigar sun farmaki 'yan sandan misalin karfe 9:00 na daren ranar Laraba, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi inda aka kashe mutum biyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.