Gudun Duniya: An Gwangwaje Dan Sanda da Kyauta Bayan Kin Karbar Cin Hancin N150m

Gudun Duniya: An Gwangwaje Dan Sanda da Kyauta Bayan Kin Karbar Cin Hancin N150m

  • Jami'in dan sanda ya samu kyautar makeken fili a birnin Abuja bayan kin karbar cin hanci har N150m daga wani dan kasuwa
  • Ibrahim Ezekiel Sini ya ce ya ki karbar cin hancin domin samun aminci a cikin zuciyarsa da kare mutuncin kansa
  • Kwamishinan 'yan sanda a Abuja, Benneth Igweh shi ya mika kyautar filin ga Sini inda ya ce ya daga kimar rundunar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Jami'in dan sanda da ya kaucewa karbar cin hancin N150m ya samu kyautar makeken fili a Abuja.

Ibrahim Ezekiel Sini ya ki amsar cin hancin N150m daga babban dan kasuwa mai suna Akintoye Akindele da ke kulle a gidan yari.

Kara karanta wannan

Limami ya shiga matsala kan zuwa aikin hajji babu izinin basarake, an yi masa barazana

Dan sanda da ya ki cin hancin N150m ya samu kyauta a Abuja
An gwangwaje dan sanda, Ibrahim Ezekiel Sini da kyautar makeken fili bayan kin cin hancin N150m. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Abuja: An ba dan sanda kyautar fili

Kwamishinan 'yan sanda a birnin Abuja, Benneth Igweh shi ya tabbatar da haka yayin mika kyautar a Abuja, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Igweh wanda ya mika filin ga dan sanda ya ce tabbas Sini ya sanya rundunar alfahari ya sake wanke su daga zarge-zargen karbar cin hanci.

Wani daga cikin wandanda suka shirya taron, Chukwuemeke Okoye ya ce ya kamata sauran jami'an rundunar su yi koyi da halin Sini, Vanguard ta tattaro.

"Halin dattaku da Sini ya nuna ba iya rundunar zai saka alfahari ba har ma da sauran wadanda suka ki jinin cin hanci a Najeriya."
"Wannan hali da ya nuna ya kamata wasu ma su yi koyi da shi musamman a irin wannan tsananin da ake ciki."
"Tabbas kin karbar cin hancin har na N150m akwai tarbiya a ciki da kuma tsoron Allah da kwarewar aiki."

Kara karanta wannan

Yayin da ake rade radin tuge shi, Sultan ya tura sako ga rundunar sojoji

- Chukwuemeka Okoye

Musabbabin ba dan sanda cin hanci

Dan kasuwa, Akindele shi ya ba Sini cin hancin N150m domin neman dakatar da bincikensa da ake yi.

An daure Akindele ne a gidan gyaran hali da ke Kuje a birnin Abuja bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an ba da cin hancin ne domin ba shi damar tserewa ketare da rubuta rahoto mai kyau game da shi.

Yan sanda sun cafke mutane 4

Kun ji cewa Rundunar 'yan sanda a Abuja ta ce ta cafke mutum hudu da ake zargi da hannu a kisan Uwem Udokwere, wani Birgediya Janar ɗin soja.

An ruwaito cewa wadanda ake zargin sun kashe Janar Udokwere a safiyar ranar Asabar a wani rukunin gidajen birnin Tarayyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel