Abuja: Asirin Waɗanda Suka Kashe Birgediya Janar Zai Tonu, an Kama Mutum 4

Abuja: Asirin Waɗanda Suka Kashe Birgediya Janar Zai Tonu, an Kama Mutum 4

  • Rundunar 'yan sanda ta cafke mutum hudu da ake zargi da kashe wani Janar ɗin soja (mai ritaya), M.J Uwem Udokwere
  • An ruwaito cewa wadanda ake zargin sun shiga har cikin gidansa da ke Abuja suka kashe shi a safiyar ranar Asabar, 22 ga watan Yuni
  • Kwamishinan 'yan sandan Abuja, Benneth Igweh ya ce har yanzu ana farautar sauran mutum biyu da ake zargi da kisan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ce ta cafke mutum hudu da ake zargi suna da hannu a kisan Uwem Udokwere, wani Birgediya Janar ɗin soja (mai ritaya).

An ruwaito cewa wadanda ake zargin sun kashe Janar Udokwere a safiyar ranar Asabar a wani rukunin gidajen birnin tarayyar.

Kara karanta wannan

Duk da ikirarin gidansa 1 tak, an gano El Rufai ya mallaki gidan $193,084 a Dubai

'Yan sanda sun kama wadanda suka kashe Birgediya Janar a Abuja
'Yan sandan Abuja sun ce an kama mutum 4 da laifin kashe Birgediya Janar (mai ritaya) Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

An kama makasan tsohon Janar a soja

Da ya ke jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, kwamishinan 'yan sandan Abuja, Benneth Igweh, ya ce har yanzu ana farautar mutane biyu, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Lahadi ne aka ruwaito jami'an 'yan sanda, bisa jagorancin CSP Victor Godfrey, suka fara bincike kan kisan tsohon sojan.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an cafke wadanda ake zargin ne ta hanyar 'bi diddigin' wayar daya daga cikinsu da ta fadi lokacin da ake bin bayan su.

Sunayen wadanda ake zargi da kashe Janar

Shugaban rukunin gidajen Sunshine Homes, inda aka kashe tsohon sojan, Odulami Ayotunde ya ce 'yan sanda sun yi masu bayani kan rahoton kama wadanda ake zargin.

"Mun je ofishin 'yan sanda domin jin inda aka kwana, sun sanar da mu wani daga cikin wadanda ake zargin ya jefar da wayarsa, sun bi diddigi har sun kama mutum hudu."

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin sama sun yi nasara kan barayin man fetur a Najeriya

- Mista Odulami Ayotunde.

Rahoton ya lissafa wadanda aka kama da suka hada da Ibrahim Rabiu (Kano), Nafiu Jamil (Kano), Aliyu Abdullahi (Zamfara) da Mohammed Nuhu (Kano).

Gobara ta tashi a cocin Christ Embassy

A wani labarin, mun ruwaito cewa gobara ta tashi gadan gadan a hedikwatar cocin Christ Embassy da ke jihar Legas a ranar Lahadi, ana dab da fara gudanar da ayyukan ibada.

Hukumar kashe gobara ta jihar Legas (LSFRS) ta bayyana cewa gobarar ta kama ne a babban dakin taro na cocin kuma ta yi barna saboda ba a kira hukumar da gaggawa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.