Gini Ya Rufta Kan Mutane 2 a Abuja, Gwamnati Ta Dauki Matakin Gaggawa
- An shiga tashin hankali a rukunin gidajen Prince and Princess da ke Abuja yayin da wani gini da ake kan ginawa ya rufta kan mutane
- An ruwaito cewa masu aikin ginin sun yi gaggawar ficewa daga cikin gidan lokacin da suka fahimci yana shirin rugujewa
- Hukumar ba da agajin gaggawa ta birnin tarayya (FEMD) ta ce jami'anta sun yi nasarar ceto mutane biyu da ginin ya fada kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An ceto mutane biyu da ransu daga ƙasan wani gini da ya rufta kansu a wani rukunin gidaje na Prince and Princess da ke gundumar Gudu, babban birnin tarayya Abuja.
Mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa ta Abuja (FEMD), Nkechi Isa ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar.
An ceto mutane 2 da gini ya rufta kansu
Nkechi Isa ta yi nuni da cewa daraktar FEMD, Misis Florence Wenegieme ta tabbatar da cewa maaika sun fice daga ginin lokacin da suka ga alamar zai rufta, in ji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai sanarwar ta ce akwai mutane biyu da suka makale a wani gida da ke bayan gidan da ya rufta, abin da ya sa jami'an ceto suka kai dauki.
Sanarwar ta ce jami'an sashen bincike da ceto na hukumar FEMD sun ɓalle tagar gidan da mutanen suke ciki, suka samawa kansu hanya tare da ceto mutanen biyu.
FEMD ta aika sakon gargaɗi ga magina
A hannu daya kuma, jaridar The Punch ta ruwaito shugabar hukumar FEMD, Misis Florence tana yi kira ga masu gini a birnin da su riƙa kiyaye dokokin gini a kowanne lokaci.
Ta nemi magina da su kasance masu yin gwaje-gwajen da ya kamata kan gine-ginen da dama akwai su kafin ace za ayi sabon aiki a kansu.
Shugabar FEMD ta jaddada cewa idan har magina suka rika kiyaye ka'idoji wajen yin gini, hakan zai taimaka wajen kare ma'aikata da ma wadanda za su zauna a ginin.
Me ke jawo yawan ruftawar gine-gine?
A zantawarmu da masani kan harkar gine-gine, Arch. Abdullahi Rabiu a Abuja, ya ce ana samun yawaitar rushewar gine-gine saboda wasu dalilai da dama.
Arch. Abdullahi ya ce ana iya samun kuskuren farko daga wanda ya zana gidan, yana mai cewa kura-kurai a wajen kayyade adadin nauyin da gini zai iya dauka na jawo ruftawarsa.
Mai zane-zanen gidan ya ce idan ba a samu matsala daga zane ba, to ana iya samun matsala daga wadanda za su yi ginin, walau kin bin tsarin zanen, ko amfani da kayan aiki marasa kyau.
Ya yi nuni da cewa kin kiyaye tsarin amfani da siminti, ruwa, yashi, duwatsu ko kuma kin yin amfani da kayan aiki masu kyau na sa gini ya rufta tun kafin ma a kammala shi.
Masanin gine-ginen ya ce mutane na amfani da wadanda basu kware ba a wajen gini saboda gudun biyan kudi masu yawa, wanda hakan ke jawo rushewar gini da asarar rayuka.
Gini ya rufta kan mutane a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani gini mai bene biyu a kasuwar Kano ya rufta ya danne ma'aikata da yara masu talla da mai siyar da abinci a titin Beiru.
Jami'an tsaro masu bada dauki da suka kunshi yan sanda, jami'an kwana-kwana, ma'aikatan SEMA da jami'an FRSC sun yi nasarar ceto mutane uku bayan sun haka rami sun ciro su.
Asali: Legit.ng