Rushewar Gini: Buhari ya jajantawa al'ummar jihar Filato

Rushewar Gini: Buhari ya jajantawa al'ummar jihar Filato

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi alhini tare da jajantawa 'yan uwan wadanda azal ta fadowar gini ta afka masu a birnin Jos na jihar Filato da a sanadiyar haka rayukan mutane 14 suka salwanta.

Rayukan mutane 14 sun salwanta a sanadiyar rushewar wani dogon gini mai hawa uku a yankin Dilimi na karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA ta bayyana.

Da yake bayyana bakin cikin sa a daren ranar Talatar da ta gabata, shugaban kasa Buhari ya zayyana yadda ya tsinci kansa cikin firgici gami da damuwa a sanadiyar wannan mummunan tsautsayi da ya auku.

Yayin jaddada cewar duk wata damuwa da ta shafi al'ummar jihar Filato shi ma ta shafe shi, shugaban kasa Buhari ya yi alhinin mutuwar wadanda suka riga mu gidan gaskiya tare da addu'ar samun waraka ga wadanda suka jikkata.

KARANTA KUMA: An kashe dalibi daga Najeriya a kasar Malaysia

Ba ya ga kwarara addu'o'i da neman samun sauki na radadin aukuwar wannan ibtila'i, shugaban kasa Buhari ya yi kira na neman dukkanin masu ruwa da tsaki da su tabbatar da ingancin gine-gine domin magance rushewar su da ta yawaita cikin kasar nan a yanzu.

A wani rahoton mai nasaba da jaridar The Punch ta ruwaito, saukar ruwan sama na mamako yayi sanadiyar rushewar wani gini da ya danne fiye da mutane arba'in yayin da rayukan mutane biyu suka salwanta makonni biyu da suka gabata a birnin Mumbai na kasar Indiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel