Sarautar Kano: Abin da Sanusi II Ya Fadawa Kungiyar Mata Masu Tafsiri a Fadarsa

Sarautar Kano: Abin da Sanusi II Ya Fadawa Kungiyar Mata Masu Tafsiri a Fadarsa

  • Yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar Kano, Kungiyar mata masu tafsiri sun ziyarci fadar Sarkin Kano
  • Mata a karkashin kungiyar da ke masallacin marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud sun kai ziyarar domin nuna goyon baya
  • Daga bisani, Muhammadu Sanusi II ya godewa matan inda ya yaba musu kan ayyukan alheri da suke yi a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kungiyar mata masu tafsiri a jihar Kano ta kai ziyarar caffan ban girma zuwa ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Kungiyar da ke masallacin marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud a Dorayi ta kai ziyarar ne domin nuna goyon bayansu.

Kungiyar mata masu tafsiri sun ziyarci Sanusi II a fadarsa a Kano
Muhammadu Sanusi II ya karbi bakwancin kungiyar mata masu tafsiri a jihar Kano. Hoto: @masarautarkano.
Asali: Twitter

Kano: Sanusi II ya karbi bakuncin mata

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Bayero: Manazarci ya hango makomar sarautar Kano bayan hukuncin kotu

A cikin wani faifan bidiyo da @SanusiSnippets ta wallafa a shafin X a yau Talata 25 ga watan Yunin 2024, matan sun yi ruwan addu'o'i ga Sarkin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin ziyarar, matan sun bayyana goyon bayansu ga Sanusi II tare da yin addu'a ta musamman ga Sarkin.

Daga bisani, sarkin ya yi godiya ga kungiyar matan bisa kyawawan ayyuka da suke yi na addini.

Sanusi II ya ba mata masu tafsiri shawara

Sarkin ya hore su da su ci gaba da wannan aikin alheri da suke gudanarwa na ilmantarwa da fadakarwa.

Ya ce abin burgewa ne kasancewarsu mata kuma ita mace makaranta ce ta musamman da yara ke fara samun tarbiya.

Daga karshe ya yi musu addu'ar samun nasara a duka ayyukan da suke yi wanda rahamar Allah ke sauka a kansa.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar jihar bayan tuge Aminu Ado Bayero.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Gingima-gingiman lauyoyi sun soki hukuncin kotu, sun zargi ƴan siyasa

Hakimai sun ziyarci sarki Sanusi ii

A wani labarin, kun ji cewa hakimai da dagatai daga duka kananan hukumomin jihar Kano 44 sun ziyarci Muhammadu Sanusi II a fadarsa.

Hakiman da dagatai daga kauyuka da dama sun ziyarci fadar ne da shugabannin riko na kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.

Musabbabin ziyarar ita ce nuna goyon baya da kuma yin mubaya'a ga Sarkin duk da dambarwa da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.