Sojoji Sun Yi Karin Haske Kan Zargin Ɗaukar Musulmai Masu Tsaurin Ra'ayi a Aiki

Sojoji Sun Yi Karin Haske Kan Zargin Ɗaukar Musulmai Masu Tsaurin Ra'ayi a Aiki

  • Rundunar sojojin Nigeria ta ƙaryata jita-jitar cewa tana daukar Musulmai masu tsattsauran ra'ayi aikin soja a Najeriya kamar yadda ake yadawa
  • Dakarun sun musanta wata murya da ake yadawa inda wani ke shawartar Musulmai su shiga aikin domin kare Musulunci
  • Hakan ya biyo bayan zargin da ake yi a cikin muryar cewa rundunar tana daukar Musulmai masu tsattsauran ra'ayi domin kare Musulunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta yi martani kan rade-radin daukar Musulmai masu tsattsauran ra'ayi aikin soja.

Rundunar ta karyata wani murya da ake yadawa kan lamarin inda ta ce babu kamshin gaskiya a ciki.

Kara karanta wannan

Ana jita jitar tsige Sarkin Musulmi, Atiku ya ba da shawara 1 ta kare martabar sarakuna

Sojoji sun yi martani kan zargin ɗaukar ƴan ta'adda aikin soja
Rundunar sojoji ta magantu kan rade-radin daukar ƴan ta'adda aikin soja. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Sojoji sun yi martani kan daukar aiki

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran rundunar, Manjo-janar Onyema Nwachukwu ya fitar a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onyema ya kuma karyata wata murya da aka ce ta soja ne inda ya ke shawarar Musulmai su shiga aikin soja domin kare Musulunci.

"Wannan an yi ne domin kawo fargaba da tsoro da kuma rudani a tsakanin jami'anmu."
"Hakan kuma zai saka fargaba da tsoro a zukatan wadanda ba Musulmai ba inda za su ji cewa rayukansu na cikin barazana."
"Dakarun sojoji sun himmatu wurin tabbatar da kwarewarsu a aiki ba tare da nuna wariya na addini ko kabilanci ba."

- Onyema Nwachukwu

Rundunar soja ta kare tsarin ayyukanta

Onyema ya ce rundunar tana gudanar da ayyukanta ne bisa tsarin doka ba wai bin wani addini daban ba ko kabilanci.

Kara karanta wannan

An kama ɗan damfara da sunan samawa mutane aikin soja, rundunar soji ta yi karin haske

Manjo-janar Onyema ya kuma shawarci al'ummar Najeriya da su yi watsi da wannan jita-jita inda ya ce zai rage musu kwarin guiwa kan sojoji.

Ƴan bindiga sun hallaka Janar a soja

A wani labarin, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun hallaka wani tsohon Birgediya-janar na soja a birnin Abuja.

Lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Lahadi da misalin karfe 3.00 na dare inda suka shiga cikin gidansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.