An Kama Ɗan Damfara da Sunan Samawa Mutane Aikin Soja, Rundunar Soji Ta Yi Karin Haske

An Kama Ɗan Damfara da Sunan Samawa Mutane Aikin Soja, Rundunar Soji Ta Yi Karin Haske

  • Rundunar sojin Najeriya ta kama wani mutum da yake damfarar mutane da sunan zai musu hanyar shiga aiki soja cikin sauki
  • Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa ne ya bayyana haka a jiya Asabar bayan kama mutumin yayin da yake kokarin karbar kudi
  • Rundunar sojin ta tabbatar da cewa an kama mutumin ne a jihar Taraba kuma ta yi kira na musamman ga daukacin masu neman aikin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cafke wani ɗan damfara da yake ƙoƙarin cutar mutane da sunan sama musu aiki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama mutumin ne a jihar Taraba yayin da ake kokarin tantance mutanen da za a dauka aikin soja.

Kara karanta wannan

Yadda kwankwaɗar kunun aya ya hallaka mutane 24, Gwamna ya dauki mataki mai tsauri

Sojojin Najeriya
Sojoji sun kama dan damfara a Taraba. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: UGC

Legit ta gano haka ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka kama ɗan damfara

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kama mutumin a jiya Asabar yayin da yake ƙoƙarin karbar kudi a hannun masu neman shiga aikin soja.

Mutumin na cikin shirya dabarar karbar kudi a hannun masu neman aiki ne sai rundunar ta yi gaggawa ta gano shi tare da cafke shi.

Rundunar ta kara da cewa cafke mutumin ya jawo kubutar da dubban masu neman aikin daga yin hasarar kudi domin ba shi da hanyar da zai sama musu aiki.

Rundunar soji ta yi karin haske

Kwamandan rundunar sojin Najeriya ta shida a Taraba, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa ya gargadi masu neman aikin da su guji mika kudi da sunan za a musu hanya.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta yi taro a Kano, ta tura buƙatarta ga 'yan jarida

Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa ya kuma tabbatar da cewa za su gudanar tantance masu neman aikin cikin adalci tare da zaben wadanda suka cancanta.

Ya kuma yi kira ga masu neman aikin da su gaggauta sanar da jami'an rundunar idan wani ya yi yunkurin karbar kudi a hannunsu.

Sojoji sun kama dan ta'adda

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kama ƙasurgumin ɗan ta'adda da ake zargi ya fitini ƙauyuka da dama a jihar Taraba da ke Arewa maso gabas.

Rahoto ya nuna rundunar ta sanar da cewa ta bi sawun ɗan ta'addar ne bayan ya aikata ta'asa a wani kauye yana ƙoƙarin neman mafaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng