Tuhumar Wulaƙanta Naira: Kotu Ta Ɗauki Mataki Kan Fitaccen Ɗan Kasuwa, Obi Cubana

Tuhumar Wulaƙanta Naira: Kotu Ta Ɗauki Mataki Kan Fitaccen Ɗan Kasuwa, Obi Cubana

  • Wata babbar kotun tarayya da ke da zama a Legas ta kori karar da hukumar EFCC ta shigar kan fitaccen ɗan kasuwa, Cubana Chief Priest
  • Wannan na zuwa ne bayan da EFCC da Cubana suka cimma yarjejeniya a bayan fage da kuma alkawarin ba zai kara wulakanta Naira ba
  • Mai shari'a Kehinde Ogundare ya umarci wanda ake tuhumar ya biya gwamnatin tarayya tarar Naira miliyan 10 kamar yadda doka ta tanada

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Legas - Wata babbar kotun tarayya da ke da zama a Legas ta umarci fitaccen ɗan kasuwa, Cubana Chief Priest ya biya gwamnati tarar N10m saboda tuhumarsa da wulaƙanta Naira.

Kara karanta wannan

EFCC ta shaidawa kotu yadda Emefiele ya yi tuwona maina wurin bada kwangilar CBN

Wannan na daga cikin yarjejeniyar da hukumar EFCC da ɗan kasuwar suka cimmawa a bayan fage, wanda Mai shari'a Kehinde Ogundare ya amince da ita.

Kotu ta yanke hukunci kan shari'ar EFCC da Cubana
EFCC da Cubana sun cimma yarjejeniya, kotu ta soke tuhumar cin zarafin Naira. Hoto: @Chiefpriiest, @officialEFCC
Asali: Twitter

Cubana da EFCC sun yi yarjejeniya

A yayin zaman kotun na yau Talata, lauyar EFCC, Bilkisu Buhari-Bala ta shaidawa kotun cewa EFCC da Cubana sun daidaita a wajen kotu, in ji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan wanda ake kara, Chikaosolu Ojukwu (SAN) ya yabawa kokarin hukumar EFCC na warware matsalar cikin lalama kuma a karamin lokaci.

Mista Ojukwu ya ce wanda ya ke karewa ya yi nadamar abin da ya aikata kuma ya sha alwashin hakan ba zata sake faruwa a nan gaba ba.

Lauyan ya kuma nemi kotun da ta rushe tuhumar da ake yiwa Cubana Chief Priest, tun da dama manufar yin yarjejeniyar kenan.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan sanatan PDP da ake tuhuma da buga takardar NYSC ta bogi

Kotu ta yanke hukunci kan tuhumar Cubana

Jaridar The Nation ta ruwaito Mai shari'a Ogundare a hukuncin da ya yanke, ya amince da yarjejeniyar da Cubana da EFCC suka kulla, kuma ya soke tuhumar.

Kulla irin wannan yarjejeniyar na kunshe ne a cikin sashe na 14 (2) na dokar da ta samar da hukumar EFCC da aka kafa a 2004.

Dokar ce ta nemi wanda ake zargin ya biya gwamnatin tarayya tarar Naira miliyan 10, tare da yin alkawarin gujewa faruwar laifin a gaba.

Atiku ya gargadi gwamnoni kan taba sarakuna

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gargadi gwamnoni jihohi daga taba masarautun gargajiya.

Atiku Abubakar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da 'yan majalisun tarayya da su yi garambawul ga kundin tsarin mulkin Najeriya domin ba da damar sanya masarautun gargajiya a cikin doka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.