Gwamnatin Tarayya za ta Sauyawa Kurkuku Mai Shekaru 200 Matsuguni

Gwamnatin Tarayya za ta Sauyawa Kurkuku Mai Shekaru 200 Matsuguni

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kammala shirin sauyawa kurkukun da aka gina shekaru 200 baya wurin zama saboda cunkosu da kuma shiga cikin mutane
  • Ministan harkokin cikin gida, Olabunmi Tunji Ojo ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa gidan da aka gina saboda mutane 340 yanzu haka na dauke da mutane 750
  • Ya bayyana damuwa kan halin da gidan ke ciki, yayin da ya jaddada cewa kurkukun kasar nan ya koma gidan gyaran hali da tarbaiyyar daurarrun da za a rika kai wa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tuni ta kammala shirin sauyawa kurkukun Keffi da ke jihar Nassarawa matsuguni saboda wasu dalilai.

Kara karanta wannan

'Bashi bai amfanar talaka', an bukaci binciken yadda Najeriya ke kashe bashin da ta ci

Daga dalilai biyu da ministan harkokin cikin gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo ya bayar akwai cunkosun wadanda ke tsare, kuma birni ya cimma gidan.

Minista
Gwamnati za ta sauyawa kurkukun Keffi matsuguni Hoto: Hon Olubunmi Tunji-Ojo
Asali: Facebook

Leadership News ta walllafa cewa Mista Tunji Ojo ya ce ginin da aka yi shi tun 1820 ya yi wa daurarrun da ke cikinsa kadan, kuma ya na cikin halin lalacewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kurkukun ya yi kadan," Minista

Kurkukun Keffi an gina shi ne domin daurarru 340, amma yanzu haka akwai mutane sama da 750 a cikinsa, kuma 605 na daga cikinsu na jiran shari'a.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji Ojo na ganin gidan gyaran halin ya yi kadan matuka, baya ga lalacewa da wani bangare na gidan ya yi.

Nigerian Tribune ta wallafa cewa da ya ke duba wani kurkukun Karshi da ake ginawa a Abuja da zai dauki daurarru 3000, ya ce ma'aikatarsa da hukumar kula da gidajen gyaran hali a Najeriya na duba matsalolin da su ka gano.

Kara karanta wannan

Kwalara na kisa a awanni, gwamnatin Kano ta yi gargadin amfani da ruwan sama

Ya jaddada cewa kurkukun kasar nan ya sauya daga wajen daure mutane kawai zuwa gidan gyaran hali da tarbiyya, saboda haka za a yi gyare-gyare domin a tabbatar da hakan.

Daurarru sun tsere daga gidan kurkuku

A wani labarin kun ji cewa daurarru uku sun tsere daga gidan gyaran hali da tarbiyya a jihar Ogun bayan sun yi nasarar tsallake katangar gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda su ka tsere an yanke masu hukunci kan mugayen laifuka da su ka hada da fashi da makami, fyade da kisan kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.