Boko Haram Sun Sace Babban Alkali da Iyalansa, Sun Shiga da Su Dajin Sambisa
- Rahotanni da ke fitowa daga jihar Borno sun yi nuni da cewa yan kungiyar Boko Haram sun sace wani babban alkali
- Babban alkalin mai suna Haruna Mshelia ya hadu da yan ta'addar ne yayin da yake tafiya kan hanyar Buratai bayan ya fito daga Maiduguri
- Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa mai shari'a Haruna Mshelia ya yi kokarin guduwa yayin da suka tare shi amma bai yi nasara ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Yan ta'addar Boko Haram sun sace daya daga cikin manyan alkalan babbar kotun jihar Borno.
Rahotanni sun yi nuni da cewa alkalin mai suna Haruna Mshelia ya hadu da ƴan ta'addar ne yayin da yake tafiya a kan hanya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a jiya Litinin, 24 ga watan Yuni a kan hanyar Buratai-Buni-Gari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Boko Haram ta sace alkali
Rahotanni sun yi nuni da cewa yan Boko Haram sun fito ne daga daji suka tsaya kan hanya yayin da alkalin ke kokarin wucewa.
Bayan alkalin ya yi kokarin kaucewa yan ta'addar sai wasu suka kara fito masa a gaba kuma suka yi nasarar kama shi.
Ina Boko Haram ta tafi da alkalin?
Yan ta'addan Boko Haram sun kama alkali Haruna Mshelia ne tare da matarsa da mai tuka masa mota, rahoton Vanguard.
Kuma majiya mai tushe ta tabbatar da cewa bayan kama su yan ta'addar sun tafi da su dajin Sambisa.
Yan sanda sun tabbatar da lamarin
Kakakin yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso ya ce sun samu rahoto cewa an kama alkalin a hanyar Biu.
ASP Nahum Daso ya tabbatar da cewa suna ƙoƙarin ganin an ceto alkalin da sauran wadanda aka kama a kan hanyar.
Sojoji sun ceto mutane a Sambisa
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Najeriya sun yi nasarar ceto wasu mutanen da ‘yan ta’adda suka sace tsawon shekaru 10 zuwa yanzu.
Rahotanni sun bayyana sabon aikin da sojojin suka fara domin tabbatar da sun kakkabe dajin Sambisa daga masu aikata ta’addanci.
Asali: Legit.ng