Ana Tsaka da Rikicin Sarauta, Kano Ta Yi Sabon Kwamishinan Ƴan Sanda, Salman Garba
- Sabon kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba ya sha alwashin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar
- CP Salman Garba ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da ya ke kama aiki bayan tafiyar tsohon kwamishinan 'yan sanda, Usaini Gumel
- Usaini Gumel wanda ya samu karin matsayi zuwa mataimakin Sufeta Janar, ya bayyana lokutan da ya sha wahalar aiki a zamansa Kano
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Pompai, Kano - Jihar Kano ta yi sabon kwamishinan 'yan sanda biyo bayan karin matsayi da CP Usaini Gumel ya samu zuwa matsayin mataimakin Sufeta Janar (AIG).
Sabon kwamishinan 'yan sandan Kano, Salman Dogo Garba, ya kama aiki ne a ranar Litinin, 24 ga watan Yunin 2024.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an gudanar da bikin bankwana da AIG Usaini Gumel a babban ofishin jami'an 'yan sanda na Pompai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Usaini Gumel ya magantu kan aiki a Kano
Da yake waiwaye kan yadda ya gudanar da aiki a Kano daga 2 ga Mayun 2023 zuwa 24 ga Yunin 2024, Gumel ya bayyana abubuwan da suka ba shi ciwon kai a jihar.
AIG Gumel ya ce zaben gwamnan jihar Kano na 2023 da ya gudana shi ya fi wahalar da shi kasancewar akwai takun sakar siyasa mai zafi daga ɓangarorin siyasar jihar.
"Kula da zaben 2023, daga ranar da aka sanar da sakamako har zuwa zuwa kotu, a matakin jihar da Kotun Koli, ya wahalar da ni sosai.
"Sannan sai rikicin sarautar Kano na baya-bayan nan wanda wasu 'yan siyasa suka so siyasantar da harkar tsaro."
- AIG Usaini Gumel.
CP Salman Dogo Garba ya dauki alkawari
Da ya ke na shi jawabin, sabon kwamishinan 'yan sandan, CP Salman Garba ya lashi takobin ba da tsaro ga lafiya da dukiyoyin al'ummar jihar Kano, inji rahoton The Punch.
CP Salman Garba ya nemi hadin kai da goyon bayan jami'an yan sandan jihar Kano da ma daukacin al'ummar jihar wajen gudanar da wannan aiki.
An karrama AIG Usaini Gumel a Kano
A yayin gudanar da wannan taro na bankwana, kungiyar 'yan jaridu masu kawo rahoto karkashin NUJ, reshen Kano, sun karrama AIG Gumel bisa namijin kokarinsa.
Haka zalika an gabatar da mika kyaututtuka ga wasu daga cikin jami'an 'yan sandan jihar bisa kokarinsu na wanzar da zaman lafiya.
Yan sanda sun mamaye fadar sarkin Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an rundunar 'yan sandan Kano sun mamaye fadar sarkin Kano Muhammadu Sanusi II tare da fatattakar'yan tauri da ke gadin sarkin.
Wannan matakin ne wasu ke kallo a matsayin wani yunkuri na mayar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero kan kujerarsa bayan hukuncin kotu da ya rusa batun tsige shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng