An Ladabta Jami’an Kotun Kano da Suka Wawushe Kudi a Asusun Banki
- Hukumar kula da harkokin shari'a a jihar Kano (JSC) ta dauki mataki kan wasu jami'an kotun majistare bayan karkatar da kudi
- Hukumar JSC ta dauki mataki kan Talatu Makama, Rabi Abdulkadir, Tijjani Saleh Minjibir da wani jami'in kotu mai suna Abdu Nasir
- Jami'in yada labaran hukumar JSC, Baba Jibo-Ibrahim ne ya sanar da lamarin ga manema labarai a yau Litinin, 24 ga watan Yuni
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Hukumar da ke kula da harkokin shari'a a jihar Kano (JSC) ta dauki mataki mai tsauri kan wasu jami'an kotu da ake zargi da badakala.
Rahotanni sun nuna cewa an zargi mutanen su hudu, Talatu Makama, Rabi Abdukadir, Tijjani Saleh Minjibir da Abdu Nasir da da aikata laifuffuka da suka shafi kudi.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa jami'an yaɗa labaran hukumar JSC ne ya sanar da lamarin a yau Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Laifin da jami'an kotu suka yi
Jami'in yada labaran hukumar JSC, Baba Jibo-Ibrahim ya tabbatar da cewa ana zargin alkalin majistare mai suna Talatu Makama da karkatar da wasu kudi zuwa asusun ajiyar bankinta.
Ita kuma Rabi Abdulkadir an zarge ta da yin sakaci da rashin yin abin da ya dace da aka nada ta yin bincike kan Talatu Makama.
Haka zalika hukumar JSC ta samu Tijjani Saleh Minjibir da rikon sakainar kashi kan wasu ayyuka da aka ba shi.
Sai kuma magatakardan babbar kotun jihar mai suna Abdu Nasir da ake zargi da sanya kudin kotu a asusun bankinsa.
Matakin da JSC-Kano ta dauka
Baba Jibo-Ibrahim ya tabbatar da cewa hukumar JSC ta dauki matakin dakatar da Talatu Makama daga aiki na tsawon shekara daya, rahoton Peoples Gazette.
Haka zalika hukumar ta dakatar da Tijjani Saleh Minjibir da Rabi Abdulkadir aiki na tsawon shekara daya.
A daya bangaren kuma, hukumar ta yiwa Abdu Nasir gargadi tare da dakatar da masa karin matsayi har sai bayan shekara daya.
An gano badakala a jihar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da gwamna Abba Kabir ya kafa kwamitin bincike kan Abdullahi Umar Ganduje, wasu takardu sun bankado yadda aka yi badakala.
Rahotanni sun nuna cewa takardun da aka gano daga kotun na zargin yadda Ganduje ya siyar da kamfanin auduga ga iyalansa ba bisa ka’ida ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng