IHR Ta Tura Soƙon Jinjina ga Jihar Kaduna kan Mayarwa Mahajjata Rarar Kudi

IHR Ta Tura Soƙon Jinjina ga Jihar Kaduna kan Mayarwa Mahajjata Rarar Kudi

  • Kungiyar manema labaran aikin Hajji mai zaman kanta (IHR) ta tura saƙon jinjina ga hukumar jin daɗin mahajjata ta jihar Kaduna
  • IHR ta tura saƙon ne biyo bayan abin kirki da hukumar jin dadin alhazan ta yi na mayarwa mahajjatan jihar Kaduna rarar kudi
  • A makon da ya wuce ne jami'in hukumar ya sanar da mayarwa mahajjatan jihar rarar kudi da ka samu wajen sayen dabbobin hadaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Hukumar jin dadin alhazan jihar Kaduna ta cigaba da samun yabo bayan yunkurin mayarwa mahajjata rarar kudi.

A satin da ya wuce ne hukumar ta sanar da mahajjatan jihar cewa sun samu saukin kudin hadaya da suka biya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki tsattsauran mataki kan masallatai da coci a Plateau, ya kakaba doka

Mahajjatan Kaduna
IHR ta yabi hukumar alhazai a Kaduna bayan dawowa mahajjata kudi. Hoto: Kaduna State Pilgrims Agency
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar manema labaran aikin Hajj mai zaman kanta (IHR) ta jinjinawa hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kaduna: Sokon IHR ga hukumar alhazai

A yau Lahadi ne kungiyar IHR ta ce ya zama dole a jinjinawa hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kaduna bisa mayar da kudi ga mahajjata.

IHR ta ce ba karamin kokari hukumar ta yi ba musamman a wannan lokacin da ake samun rudani kan kudin hadaya sosai.

Har ila yau, IHR ta ce hakan zai karawa mahajjatan Kaduna karfin gwiwa da aminta da jami'an aikin Hajji a kowane lokaci.

IHR: 'Jihar Kaduna abin koyi ce'

Kungiyar IHR ta yi kira ga sauran jihohi da su yi koyi da abin da jami'an jihar Kaduna suka yi na nuna gaskiya, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Ba a gama da rigimar sarautar Kano ba, Gwamna ya yi dokar dakile tasirin sarakuna

IHR ta ce hakan yana da muhimmanci musamman ga jihohin da suka karbi kudin hadaya sama da na Kaduna amma ba a ji sun yi wani bayani ba.

Hukumar jin daɗin alhazan jihar Kaduna ta dauki aniyar mayarwa mahajjatan jihar $50 biyo bayan sauƙin da suka samu na kudin hadaya.

Mahajjata sun fara dawowa gida

A wani rahoton, kun ji cewa bayan shafe akalla wata daya a kasa mai tsarki suna gudanar da aikin Hajji, alhazan Najeriya sun fara dawowa gida

Jirgin farko na alhazan ya iso gida a ranar Asabar, misalin karfe 9:42 na dare a filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello, Birnin Kebbi a Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng