Dubun wasu masu yi wa jama’a kutse cikin asusun banki ta cika a hannun SARS

Dubun wasu masu yi wa jama’a kutse cikin asusun banki ta cika a hannun SARS

Mafi yawan jama’a yanzu su na rike da wayoyin salula na zamani. Babu shakka ana samun wasu Miyagu da kan yi amfani da wayoyi domin sace kudin Bayin Allah daga cikin akawun din su.

Kwanan nan ne dubun wani ‘dan shekara 31 da haihuwa ta cika bayan da jami’an SARS su kayi ram da shi a Legas. Sunan wannan Matashi da ake zargi da satar kudin jama’a. Dare Oladimeji.

Dare Oladimeji, wanda bai dade da dawo Najeriya ba, ya bayyana cewa su kan yin amfani da layin wayar mutum, su shiga cikin asusun bankinsa, har ta kai su sace masa kudi ko da an rufe wayar.

Karshen Dare Oladimeji ya zo ne bayan ya saci N200, 000 daga akawun din wani mutumi a Idi-Oro da ke cikin Garin Legas. Oladimeji ya bayyana duk yadda su ke bi wajen wannan danyen aiki.

Wannan Saurayi mai suna Oladimeji yake cewa yana samin bayanai game da wadanda yak e damfara ne ta hanyar yanar-gizo.

KU KARANTA: Tsohon Ministan shari’an Najeriya zai fuskanci tuhuma a gaban NBA

Ga dai abin da ya ke fada:

“Da layin waya watau SIM na ke amfani wajen satar kudi. Da zarar na samu wani layi, sai in daura shi cikin kowace karamar waya na samu. Sai in yi kokarin gano bankunan da mai layin ya ke amfani da su…”

"Misali idan mutum ya na amfani da Bankin GTB ne, sai in latsa *37*100#. Idan akwai kudi a akawun din, sai in sayi katin waya daga bankin sa. Daga nan kuma zan gane adadin kudin da ke cikin asusun mutum, sai in sace…”

Wannan Matashi ya cigaba da cewa:

“Mu na jefa kudin ne cikin akawun din wasu Bayin Allah dabam, daga can kuma sai mu sulale da kudin…”

Oladimeji ya kara da cika-baki yana fadin:

“Rufe waya bai hana mu satar kudi domin kuwa da layi mu ke amfani, don haka abin da ke hana mu satar kudi daga asusun mutum shi ne idan har ya rufe layinsa, wanda mutane da-dama ba su yi.”

Saurayin mai shekara 31 ya kuma bayyana cewa ya shiga wannan harka ne bayan dawowarsa Najeriya daga Birnin Dubai na kasar UAE. Oladimeji yace a lokacin asarar kudi ce ta hau kansa don haka ya koma wannan mugun aiki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel