Yadda Ma’aikacin Bankin Ya Yi Karyar 'Yan Bindiga Sun Sace Shi Saboda Bashin Naira miliyan N1.7
- Jami'an tsaro sun kama wani matashi mai suna Olumide Openaike, wanda ma'aikacin banki ne a jihar Ogun
- An tattaro cewa Openiake ya yi karyar 'yan bindiga sun sace shi saboda rashin iya biyan bashin da ake binsa na naira miliyan 1.7
- Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da cewa an shawo kan lamarin kuma wanda ake zargin yana tsare
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da cewar Olumide Openaike, ma'aikacin bankin Kemta Oloko, wanda aka sanar da batansa da kuma gano shi a Mokwa, jihar Neja, shi ya kitsa garkuwa da kansa.
An sanar da hakan ne bayan gano cewa lamarin wani shiri ne da nufin dauke hankali daga bashin da ake Olumide na naira miliyan 1.7.
SP Omolola Odutola, kakakin 'yan sandan jihar, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Talata, 30 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me matar ma'aikacin bankin ta sanar da midiya?
Temitope, matar ma'aikacin bankin, ta sanar da kafofin watsa labarai batun sace Olumide a ranar 17 ga watan Janairu yayin da yake hanyarsa ta zuwa wajen aiki.
Jaridar Punch ta nakalto Temitope tana cewa:
"Ina farin cikin sanar da ku cewa an gano mijina a wani wuri da ake kira Mokwa a jihar Neja. Ya kira ni a ranar Talata da rana.
"Ya karbi waya ne daga wani mazaunin yankin saboda ya ce wadanda suka sace shi sun karbe wayarsa.
"Sai muka fada masa cewa ya kai rahoto ofishin 'yan sandan can, jami'in 'dan sandan da ke bakin aiki wanda ya yi magana da mu ya ce yana a Mokwa."
Ta tuna cewa an turawa mijin nata kudi domin a dawo da shi Ibadan daga jihar Neja, inda ya kwana a gidan yan uwansa kafin ya ci gaba da tafiyarsa zuwa Abeokuta.
'Yan sanda sun bayyana mataki na gaba
Rundunar 'yan sanda a daya bangaren, ta bayyana rahoton sace ma'aikacin bankin a matsayin zamba cikin aminci.
Kakakin 'yan sandan ya ce:
"Eh, rundunar 'yan sandan ta gano cewa ma'aikacin bankin, Olumide Openaike, ya kitsa garkuwa da kanshi ne kan bashin naira miliyan 1.7. Kudin mallakin bankin da yake aiki ne.
"Abun da ya faru shine cewa wani kwastama yana dawo da kudin bankin amma Openaike yana ta karkatar da shi zuwa ga amfanin kansa.
"Ya ce sai ya shiga damuwa sannan ya kitsa garkuwa da kansa. Yanzu haka yana tsare a hannun 'yan sanda."
'Yan sanda sun kama mata da miji
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wasu ma’aurata da ake zargi da yin garkuwa da kansu da nufin karbar kudin fansa har naira miliyan biyar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, yayin da ya gargadi ‘yan kasar da su guji yin garkuwa da kansu.
Asali: Legit.ng