'Yan Bindiga Sun Shiga Har Gida Sun Sace Babban Malamin Addini

'Yan Bindiga Sun Shiga Har Gida Sun Sace Babban Malamin Addini

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi aika-aika a jihar Zamfara bayan sun sace wani babban limamin cocin Katolika a birnin Gusau
  • Ƴan bindigan sun shiga har cikin gida ne sannan suka yi awon gaba da Rev. Fr. Mika Sulaiman a ranar Asabar, 22 ga watan Yunin 2024
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa an tura jami'ai domin bin sahun ƴan bindigan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun yi garkuwa da limamin cocin St. Raymond Catholic Church Damba, da ke Gusau, jihar Zamfara, Rev Fr. Mika Sulaiman.

Ƴan bindigan sun sace malamin addinin ne a ranar Asabar, 22 ga watan Yunin 2024.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarauta, ƴan bindiga sun kai hari Masallaci, sun sace basarake

'Yan bindiga sun sace fasto a Zamfara
'Yan bindiga sun sace babban fasto a Zamfara Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Yadda ƴan bindiga suka sace fasto

Muƙaddashin shugaban ɗarikar Katolika na Sokoto, Very. Rev Fr. Nuhu Iliya a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar ya tabbatar da sace Mika Sulaiman, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Cike da baƙin ciki a zukatanmu, muna sanar da jama’a game da sace ɗaya daga cikin limamanmu, Rev. Fr. Mika Sulaiman."
"Wannan abin baƙin cikin ya faru ne da sanyin safiyar yau, Asabar, 22 ga watan Yuni, 2024 a gidansa.
"Fr Mika Sulaiman shi ne limamin cocin St. Raymond Catholic Church Damba, da ke Gusau, jihar Zamfara."

- Fr. Nuhu Iliya

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Lokacin da Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kakakin ƴan sandan ya ce an yi garkuwa da Mika Sulaiman ne da misalin ƙarfe 3:00 na daren ranar Asabar a gidansa da ke unguwar Damba a Gusau.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar gwamna, sun hallaka mutum 2

"Eh tabbas lamarin ya auku, amma ba a sanar da ƴan sanda da wuri ba. Yana zaune ne shi kaɗai a gidansa wanda yake a can bayan gari."
"Mun tura jami'an tsaro waɗanda suka bi sahun bayan ƴan bindiga kuma Insha Allah za a kuɓutar da shi."

- ASP Yazid Abubakar

Ƴan bindiga sun hallaka mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa an tabbatar da mutuwar mutum shida yayin da wasu da dama kuma aka yi garkuwa da su a lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a yankin Bauda da Chibiya a gundumar Maro da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng