Ana Bikin Sallah, ’Yan Bindiga Sun Tafka Kazamar Ta’asa a Sokoto, Sun Sheke Mutum 10

Ana Bikin Sallah, ’Yan Bindiga Sun Tafka Kazamar Ta’asa a Sokoto, Sun Sheke Mutum 10

  • Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kai hari wani kauye a jihar Sokoto, inda suka kashe kuma suka sace mutane da dama da sanyin safiyar Lahadi
  • Maharan sun farmaki kauyen Dudun Doki a karamar hukumar Gwadabawa ta jihar, suka kashe mutane sama da goma, kamar yadda aka ruwaito
  • Legit.ng ta ruwaito cewa, har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan lamarin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Sokoto - Rahotannin da ke fitowa na cewa da safiyar Lahadi, 16 ga Yuni, wasu 'yan bindiga sun kai hari wani kauye a jihar Sokoto.

An rahoto cewa, tsagerun sun kashe mutane da yawa kuma sun sace wasu a lokacin wannan harin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari sakatariyar ƙaramar hukuma, sun tafka babbar ɓarna

An farmaki jama'a a Sokoto ana gobe sallah
An hallaka mutum 10 a Sokoto washe garin sallah
Asali: Original

Mutane 10 sun mutu, da dama sun bata a jihar Sokoto

An samu labarin cewa maharam sun farmaki kauyen Dudun Doki a karamar hukumar Gwadabawa ta jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane fiye da goma kuma suka sace mutane da yawa a wajen karfe 1.30 na dare, rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan harin ya zo ne a daidai lokacin da Musulmai a fadin kasar nan ke shirin gudanar da bikin babbar Sallah, wato Eid Al-Adha, a yau, Lahadi, 16 ga Yuni.

'Yan sanda basu ce komai ba

Ranar Arfa, wanda ke gabatar da bikin sallah, ta kasance ranar Asabar, 15 ga Yuni.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, har yanzu ba a samu wata sanarwa daga rundunar 'yan sandan jihar game da harin ba.

Jihar Sokoto na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da ke yawan fuskantar hare-hare daga tsagerun ‘yan bindiga masu sata da kasha jama’a.

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya sun kwamushe mutum 18 bisa karya dokar aikin Hajji

An kashe 'yan sa-kai a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun hallaka akalla jami’an 'yan sa-kai na CJTF guda tara a wani mummunan hari a jihar Sokoto.

'Yan bindiga sun hallaka 'yan sa-kan ne a wani harin kwanton bauna da suka kai musu wanda ya kuma yi sanadiyyar raunata jami'an da ba a tantance adadinsu ba.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa 'yan bindigan sun kuma yi awon gaba da wasu jami’an 'yan sa-kan na CJTF guda uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.