Hadimin Buhari Ya Ja Kunnen Abba Kan Yunkurin Ruguza Fadar Aminu a Nassarawa

Hadimin Buhari Ya Ja Kunnen Abba Kan Yunkurin Ruguza Fadar Aminu a Nassarawa

  • Bashir Ahmaad bai goyon bayan Abba Kabir Yusuf a kan shirin ruguza wani bangare a fadar Sarki da ke Nassarawa
  • Hadimin na tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai dace a kashe dukiyar al’umma a wannan aiki ba
  • A maimakon a kirkiro wani sabon rushe-rushe, Malam Bashir Ahmaad ya ba gwamnatin Kano shawarar inganta ilmi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Bashir Ahmaad ya yi shekaru kusan takwas yana aiki da Muhammadu Buhari a Aso Villa, ya yi kira ga Abba Kabir Yusuf.

Mai taimakawa tsohon shugaban na Najeriya ya ba gwamnan jihar Kano shawarar ya bi a sannu a kan rikicin masarautar da ake yi.

Sarki Muhammadu Sanusi
Bashir Ahmaad ya ba Gwamnan Kano shawara kan rikicin masarautar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Shawarar da Bashir Ahmaad ya ba Abba

Kara karanta wannan

Lauya ya ci gyaran gwamna, ya fassara hukuncin Alkali a shari’ar masarautar Kano

Shawarar Bashir Ahmaad ta zo ne a X awanni bayan ya ji gwamnatin NNPP ta na yunkurin rusa bangaren fadar Sarki da ke Nassarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kirkiro wannan aiki ne da nufin fitar da Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero daga karamar fadar.

Sarautar Kano: An yiwa Bashir Ahmaad ca!

Mutane musamman mabiya Kwankwasiyya sun caccaki matashin ‘dan siyasar, suna zargin shi da yin tsit lokacin Dr. Abdullahi Ganduje.

Masu sukar Bashir Ahmaad sun ce bai yi irin wannan kira a lokacin da gwamnatin Ganduje ta tsige Muhammadu Sanusi II a 2023 ba.

A lokacin da Abba Kabir ya ruguza sababbin masarautu, Bashir Ahmaad wanda ya fito daga garin Gaya ya ce ba su ji dadin hakan ba.

Sarki Gaya, Aliyu Ibrahim yana cikin wadanda sabuwar dokar masarautar 2024 ta shafa.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abba Hikima ya magantu kan sahihin Sarkin Kano, ya jero dalilai

Kiran Bashir Ahmaad ga Gwamna Abba

"A ra’ayina, gwamnatin jihar Kano ta guji amfani da dukiyar al’umma wajen rusawa da sake gina fadar Sarki da ke Nassarawa."
"Wannan ba shi ne abin da yake da muhimmanci ga jiharmu ba yanzu."
"A maimakon haka, kudin za su fi tasiri idan aka karkatar da su wajen shawo kan bangaren ilmin da aka ayyanawa dokar ta baci a jihar. "

- Bashir Ahmaad

Idahosa ya jinjina farin jinin Kwankwaso

A baya an ji labarin cewa Bishof Isaac Idahosa ya fadi sirrin farin jinin Rabiu Musa Kwankwaso ganin yadda ya samu karbuwa a Kano.

‘Dan takarar mataimakin shugaban kasar na NNPP ya ce kyau ‘yan siyasa su yi koyi da Kwankwaso ta hanyar alaka maikyau da talaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng