Kwankwaso Ya ba Abokin Takararsa a NNPP Mamaki a Bikin Babbar Sallah a Kano

Kwankwaso Ya ba Abokin Takararsa a NNPP Mamaki a Bikin Babbar Sallah a Kano

  • Taron salla babba da Rabi'u Musa Kwankwaso ya gudanar a gidansa da ke Kano ya dauki hankalin tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a NNPP, Bishof Isaac Idahosa
  • Bishof Idahosa ya bayyana taron jama’ar da su ka zo domin nuna goyon baya ga Sanata Kwankwaso da cewa wata alama ce da ke nuna halayya ta gari da shugabanci mai kyau
  • Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasar na ganin irin wannan halayya ta jan talakawa a jika ya kamata sauran shugabanni a Najeriya su koya domin karfafa alaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Bishof Isaac Idahosa ya yaba da yadda ya ga tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ke mu’amalantar jama’a.

Kara karanta wannan

"Kalamanka ba su dace da shugaba ba," Peter Obi ya caccaki Tinubu kan talauci a Najeriya

Bishof Idahosa ya bayyana haka ne bayan ganin yadda magoya baya su ka tarbi Sanata Kwankwaso yayin bikin sallah babba a Kano.

Kwankwaso
Bishof Idahosa ya yaba da alakar kwankwaso da sauran jama'a Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Leadership News ta wallafa cewa tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasar na ganin irin wannan alaka mai karfi na nuni da shugabanci na gari da jan jama’a a jika daga shugaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ku yi koyi da Kwankwaso,” Idahosa

Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Bishof Isaac Idahosa ya shawarci shugabanni a Najeriya su yi kokarin gina ingantacciyar alaka mai kwari da takalawansu.

Ya bayyana haka ne bayan dandazon magoya bayan darikar siyasar kwankwasiyya sun taya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar zagoyar sallah babba a gidansa da ke Kano.

Daily Trust ta wallafa cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya gudanar da taron sallah a gidansa da ke Miller road inda ya samu halartar daruruwan magoya baya daga ciki da wajen jihar.

Kara karanta wannan

Sallah: Atiku ya kai ziyara ga IBB da Janar Abdulsalami a Minna, hotuna sun bayyana

Buga Galadima ya gargadi Tinubu kan Kwankawso

A wani labarin kun ji cewa jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima ya gargadi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan illar da jagoran kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso zai iya yiwa siyasarsa.

Buba Galadima ya fadi ra’ayinsa ne yayin da ake dambarwar masarautar Kano, kuma ya na ganin idan Tinubu bai bi siyasar Kano a hankali ba, zai lalata damarsa ta sake zama shugaban kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.