Kungiyoyin ma'aikatan jami'o'i NASU da SSANU sun sanar da gobe ranar shiga yajin aiki
- Bayan ASUU, sauran ma'aikatan jami'o'in Najeriya gaba daya sun shiga yajin aiki
- Wadannan ma'aikata sun hada da masu shara, masu gadi, sakatarori da masinjoji
- Hakazalika akwai manyan ma'aikatan jami'a wanda suke tafiyar da harkokin jami'a
Kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'in Najeriya (SSANU) da ma'aikata maras koyarwa (NASU) sun umurci dukkan mambobinsu dake jami'o'in Najeriya su shiga yajin aiki daga gobe Juma'a.
Shugabannin kungiyoyin biyu sun bayyana hakan ne a wasikar da suka aikewa shugabannin rassa a fadin Najeriya ranar Alhamis, The cable ta ruwaito.
Shugaban kungiyar SSANU, Mohammed Ibrahim da sakataren NASU, Peters Adeyemi, suka rattafa hannu kan takardar.
Wani sashen wasikar yace, "Dubi ga sakamakon ganawarmu, ana umurtan shugabannin NASU da SSANU na rassa su fara ganawa da mambobinsu domin musu bayani kan sakamakon ganawar da kuma shawarar da muka yanke."
"A yanzu dai, mun shiga yajin aiki daga karfe 12 na daren ranar Juma'a, 5 ga watan Febrairu, 2021."
KU KARANTA: Olonisakin, Buratai, Ibok-Ete Ibas da Siddique za su zama Jakadu a kasashen waje
DUBA NAN: Shugaba Buhari ya tsawaita wa'adin IGP Adamu da watanni 3
A bayan kungiyoyin sun yi barazanar shiga yajin aiki kan manhajar biyan albashin ma'aikata na IPPIS da kuma yadda za'a raba kudi bilyan 40 da gwamnati ta baiwa ASUU.
Hakazalika sun ambaci rashin biyansu albashi bisa yarjejeniya da kuma kudin fanshon wadanda sukayi ritaya.
Domin hana ma'aikatan shiga yajin aikin, gwamnatin tarayya ta gana da shugabannin kungiyoyin ranar Talata.
Amma sun tashi baran-baran inda kungiyoyin suka ce ba'a amsa bukatunsu biyar da suka gabatar ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng