Bello Turji Ya Fadi Yadda Ta’addanci Ya Fara a Arewa, Ya Jefa Tsohon Gwamna a Matsala

Bello Turji Ya Fadi Yadda Ta’addanci Ya Fara a Arewa, Ya Jefa Tsohon Gwamna a Matsala

  • Ƙasurgumin ɗan ta'adda, Muhammad Bello Turji ya bayyana yadda aka fara ayyukan ta'addanci a Arewa maso yammacin Najeriya
  • Ɗan ta'addan ya ce tun asali suna zaman lafiya a yankin amma sai wasu abubuwa suka faru wanda sune suka jawo barkewar ta'addanci
  • Bello Turji ya bayyana haka ne bayan wani mutum ya masa tambaya a kan ya bayar da tarihin ta'addanci a yankin a matsayinsa na shugaba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Jagoran 'yan ta'adda a Arewa maso yammacin Najeriya, Bello Muhammad Turji ya bayyana abin da ya jawo ta'addanci a yankin.

Bello Turji ya zargi tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yariman Bakura da ɗaukan matakin da ya tayar da fitinar.

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Aminu: An fara zaman ɗari ɗari a Kano bayan hukuncin da kotu ta yanke

Bello Turji
Bello Turji ya fadi abin da ya jawo suka fara ta'addanci a Zamfara. Hoto: L J Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan ne cikin wani bidiyo da Bello Turji ya amsa tambaya kamar yadda Price Abdulmalik Shehu Sfada ya wallafa a kafar Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Turji ya ce da farko ana lafiya

A cikin bidiyon, Bello Turji ya ce a farkon lamari ana zaman lafiya tsakanin Hausawa da Fulani a yankunan jihar Zamfara.

Turji ya ce ana cikin zaman lafiya sai aka yi zabe, Allah ya ba Alhaji Ahmed Sani Yarima nasarar zama gwamna a jihar Zamfara.

Yarima ya kawo shari'a Zamfara

'Dan ta'addan ya yi ikirarin Ahmed Sani Yariman Bakura ya kirkiro shari'a a Zamfara ne domin ya muzgunawa 'yan ƙabilar Fulani.

Saboda haka ne ma ya ce an fara yanke hannun Bafulatani da ya yi sata amma ba a kara hukunta wani a fadin jihar Zamfara ba.

'Yan banga sun sa Fulani a gaba

Kara karanta wannan

Ana cikin rigimar sarautar Kano, miyagu sun yi ta'asa har da jikkata yan sanda

Biyo bayan yanke hannun Bafulatani ne Bello Turji ya ce sai yan banga da yan sa kai suka rika cin karensu babu babbaka a kan Fulani.

Bello Turji ya ce a lokacin maimakon gwamnati da sauran al'umma su dakatar da su amma sai kowa ya kawar da kai.

Kuma a karkashin haka ne suma suka dauki makami domin kare kansu da samawa yan uwansu 'yanci.

Bello Turji ya sako mutane

A wani rahoton, kun ji cewa hatsabibin shugaban ƴan bindigan nan Bello Turji ya sako wasu mutum 20 da yaransa suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.

A cewar mutanen da aka sako ɗin, Bello Turji ya bayar da umarnin sako su ne saboda ƙoƙarin sulhu da wasu jami'an gwamnati daga Abuja suka fara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng