Rancen Dala Biliyan 1.5: Manyan Dokokin da Bankin Duniya Ya Kafawa Najeriya

Rancen Dala Biliyan 1.5: Manyan Dokokin da Bankin Duniya Ya Kafawa Najeriya

Abuja - Bankin Duniya ya ce zai iya soke rancen dala biliyan 1.5 da ya shirya ba Najeriya idan kasar ta gaza cika wasu sharudda na musamman da aka tanada a cikin yarjejeniyar karbar kudin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bayanin hakan ya fito ne daga cikin wani daftarin yarjejeniyar karbar rancen kudin domin aiwatar da shirin bunkasa tattalin arzikin Najeriya (RESET) karkashin tsarin DPF.

A cewar wani ɓangare na daftarin; "Najeriya ba za ta iya cirar kudi daga asusun ajiyar bashin ba har sai da amincewar bankin duniyar."

Bankin duniya ya yi magana kan ba Najeriya rancen kudi
Bankin duniya ya kafawa Najeriya dokoki kafin ya ba ta rancen dala biliyan 1.5. Hoto: Bola Ahmed Tinubu, World Bank
Asali: Facebook

Najeriya ta samu bashin Bankin duniya

Wannan daftarin yarjejeniyar yana dauke da sa hannun ministan kudin Najeriya, Wale Edun da daraktan bankin duniya na ƙasa, Taimur Samad, inji rahoton Tribune Online.

Kara karanta wannan

Badaƙalar Emefiele: An gano yadda mutane 4 suka kasafta $6.2m da aka sata daga CBN

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda aka ruwaito a baya, an raba bashin dala biliyan 1.5 zuwa gida biyu: Bashin dala miliyan 750 domin shirin IDA da kuma dala miliyan 750 domin shirin IBRD.

Bankin duniya ya kafawa Najeriya sharuda

Ga jerin manyan sharudda uku da bankin duniya ya kafawa Najeriya kafin ya ba ta rancen kudin.

1. Dokar kai tsaye daga shugaban ƙasa

Bankin ya nemi Najeriya da ta tabbatar duk wasu kudade da za a tura asusunta, ciki har da na danyen mai da gas da aka siyar, an tura kudin a farashin da ake canja dala a lokacin.

2. Garambawul ga dokar harajin VAT

Bankin duniya ya nemi gwamnatin Najeriya ta mika wa majalisar tarayya sabuwar dokar harajin VAT, tare da ƙara harajin zuwa kashi 12.5 zuwa shekarar 2026.

3. Sabunta dokar shirin ba ta tallafi

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya sun kwamushe mutum 18 bisa karya dokar aikin Hajji

Bankin duniya ya nemi gwamnatin Najeriya da ta mikawa majalisar tarayya wani sabon kudirin doka da zai yi garambawul ga shirin ba da tallafi ga 'yan Najeriya.

Tsarin biyan bashin shirin IDA

An tsara cewa za a rika biyan bashin dala miliyan 750 na shirin IDA a ranakun 15 ga Afrilu da 15 ga Oktoba na kowace shekara, kuma za a fara biya daga 2030 har zuwa 2036.

Tsarin biyan bashin shirin IBRD

An tsara za a rika biyan bashin dala miliyan 750 na shirin IBRD a ranakun 15 ga Afrilu da 15 ga Oktoba na kowacce shekara, kuma za a fara biya daga 2035 a kammala a 2048.

Kotu ta rusa kananan hukumomi 33

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotu ta rusa dokar da ta kirkiri karin kananan hukumomi 33 a jihar Ondo.

A watan Satumbar 2023, marigayi Rotimi Akeredolu, tsohon gwamnan Ondo, ya sanya hannu kan dokar bayan amincewar majalisa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel