Gwamnatin Bola Tinubu Ta Bayyana Ranakun Hutun Babbar Sallah a Najeriya

Gwamnatin Bola Tinubu Ta Bayyana Ranakun Hutun Babbar Sallah a Najeriya

  • Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Litinin da Talata, 16 da 17 ga watan Yuni a matsayin hutun babbar Sallah ta bana 2024
  • Ministan harkokin cikin gida, Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan ranar Jumu'a, ya kuma taya ɗaukacin al'ummar Musulmi murna
  • Ya roƙi musulmai su yi koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (Tsira da aminci su tabbata a gare shi) na kyautatawa da kaunar zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu ta bayar da hutun kwanaki biyu ga ma'aikata domin bikin Babbar Sallah.

Gwamnatin ta ayyana ranakun Litinin 17 da Talata 18 ga watan Yuni, 2024 a matsayin ranakun da babu aiki domin shagalin Eid El-Kabir ta bana.

Kara karanta wannan

Jigon APC, Salihu Lukman ya nakasa jamiyyar bayan ya yi murabus, ya jero dalillai

Ministan cikin gida, Tunji-Ojo.
Babbar Sallah: Gwamnatin tarayya ta bada hutun ranar Litinin da Talata Hoto: Dr. Olubunmi Tunji-Ojo
Asali: Twitter

Ministan harkokin ciki gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan ranar Jumu'a, 14 ga watan Yuni, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta taya musulmi murna

Tunji-Ojo ya taya daukacin al'ummar musulmi na gida da na kasashen waje murnar wannan rana ta idin layya.

Ministan ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da su ci gaba da yin koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW) na zaman lafiya, kyautatawa da sadaukarwa.

A rahoton Daily Trust, Tunji-Ojo ya bukace su da su yi amfani da Sallar Eid-el-Kabir wajen yi wa kasar nan addu’ar samun hadin kai, ci gaba da zaman lafiya.

Ministan ya bada tabbacin cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta dukufa kuma ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Jerin ranakun da Musulmai za su yi hutu a watannin Yuni/Yulin 2024

Yayin da yake ƙara yiwa Musulmai fatan alheri da taya murna, Tunji-Ojo ya buƙaci ɗaukacin ƴan Najeriya su yi ƙoƙarin saita ƙasar nan domin ƴaƴansu masu tasowa.

Babbar sakatariyar ma'aikatar cikin gida, Dr Aishetu Ndayako, ta fitar da wannan sanarwa a madadin minista Tunji-Ojo.

Sallah: Buni ya biya albashin Yuni

A wani rahoton kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayar da umarnin a biya ma'aikata albashin watan Yuni gabanin ranar Babbar Sallah.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da babban sakataren ofishin shugaban ma'aikatan jihar Yobe Alhaji Bukar Kilo, ya fitar a madadin shugaban ma'aikata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262