Hukumar NAHCON Ta Ba Alhazan Najeriya Umarni Yayin da Suke Shirin Dawowa Gida

Hukumar NAHCON Ta Ba Alhazan Najeriya Umarni Yayin da Suke Shirin Dawowa Gida

  • Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanya doka ga mahajjata kan ɗauko ruwan Zamzam daga ƙasa mai tsarki
  • Hukumar ta haramtawa mahajjatan ɗauko ruwan Zamzam yayin da suke dawowa gida Najeriya daga Saudiyya bayan kammala aikin Hajji
  • NAHCON ta kuma ba da tabbacin cewa za a fara jigilar Alhazan ne zuwa gida Najeriya a ranar 22 ga watan Yunin 2024 kamar yadda aka tsara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Saudiyya - Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta haramtawa maniyyatan Najeriya ɗaukar ruwan Zamzam yayin da suke dawowa daga ƙasar Saudiyya. 

Muhammad Sanda, shugaban ɓangaren kula da jigila na hukumar ta NAHCON ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na bayan Arafat a birnin Makkah ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Wani Alhaji ya fito da ƙimar Najeriya a lokacin da ya tsinci maƙudan daloli a Madinah

NAHCON ta hana Alhazai yin tsarabar ruwan Zamzam
Hukumar NAHCON ta hana Alhazai dauko ruwan Zamzam Hoto: @Nigeriahajjcom
Asali: Twitter

Mohammed Sanda ya fayyace cewa kowane mahajjaci zai samu lita biyar na ruwan Zamzam bayan ya iso, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe Alhazan Najeriya za su dawo?

Ya ƙara da cewa za a fara jigilar maniyyatan zuwa gida Najeriya ne a ranar 22 ga watan Yuni, inda jirage uku za su riƙa tashi daga ƙarfe 6:00 na safe, ƙarfe 10:00 na safe da ƙarfe 10:00 na dare a kullum.

Jiragen za su fara yin jigilar Alhazai daga jihohin Kebbi, Nasarawa, da kuma babban birnin tarayya (FCT) bisa tsarin waɗanda suka fara zuwa su fara dawowa.

Ka'idojin da aka ba Alhazan Najeriya

Shugaban ɓangaren jigilar ya kuma sake nanata ƙayyade kayan da kowane mahajjaci zai ɗauka na kilogram 40.

Ya buƙaci mahajjata da sauran masu ruwa da tsaki da su bi tsare-tsaren domin gujewa samun matsala a filin jirgin sama

Kara karanta wannan

Rai bakon duniya: Wani Alhaji daga Najeriya ya riga mu gidan gaskiya a Saudiyya

Muhammed Sanda ya kuma yi nuni da cewa dukkanin mahajjatan za su yi kwanaki 38 ne a ƙasa mai tsarki.

Gwamna Bala ya caccaki hukumar NAHCON

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya caccaki hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) kan aikin Hajjin bana na shekarar 2024.

Gwamna Bala Mohammed ya nuna damuwa kan yadda hukumar ta ba mahajjatan kunya a Saudiyya ganin yadda ta ke tafiyar lamarin a bana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel