Yanzun nan: Buhari ya kaddamar da hukumar cigaban arewa maso gabas (NEDC)

Yanzun nan: Buhari ya kaddamar da hukumar cigaban arewa maso gabas (NEDC)

-Buhari ya kaddamar da sabuwar hukuma domin cigaban arewa maso gabashin Najeriya

-Janar Paul Tarfa mai ritaya shine zai kasance shugaban wannan kungiya

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da hukumar cigaban yankin arewa maso gabas wato NEDC. Kaddamar da wannan hukuma yazone gabanin ganawar majalisar zartarwa wanda akeyi a ko wane mako ranar Laraba.

Shugaban wannan sabuwar hukuma shine Paul Tarfa wani tsohon Manjo-janar mai ritaya. Anyi wannan taron na kaddamarwa ne a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Yanzun nan: Buhari ya kaddamar da hukumar cigaban arewa maso gabas (NEDC)
Yanzun nan: Buhari ya kaddamar da hukumar cigaban arewa maso gabas (NEDC)
Asali: Facebook

KU KARANTA:Ya dace a canja dukkan shugabanin hukumomin tsaro na Najeriya - ADP

Sauran mambobin hukumar sun hada da: Mohammed Alkali (Daraktan gudanrwa), Musa Yashi (Daraktan kula da jama’a), Muhammad Jawa, Omar Mohammed, David Kente, Asmau Muhammad, Benjamin Adanyi, OLawale Oshun, Ekechi T. da Obasuke McDonald.

Da yake jawabi akan kaddamar da wannan hukumar, Buhari yace bude wannan hukuma na daya daga cikin kudurorinsa na tabbatar da cigaban yankin arewa maso gabas. Kasancewar yankin ya lalace sakamakon matsalar Boko Haram.

Bugu da kari, kaddamar da wannan hukuma ya kasance tukwici bisa goyon bayan da yankin na arewa maso gabas suka bamu a lokacin zaben shekarar 2015 da 2019.

A domin cigaban wannan hukumar ta yadda zata fara aiki ba tare da cikas ba, shugaba kasan yace an tanadar masu N10bn daga cikin kasafin kudin wannan shekara.

Ya kuma nemi wannan hukuma da ta bincike halin da jihohin wannan yankin suka tsinci kansu a sanadiyar rikice-rikicen kungiyar Boko Haram.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng