Sarkin da Ya fi Daɗewa a Sarauta a Arewa Ya Rasu, Bola Tinubu Ya Tura Saƙon Ta'aziyya

Sarkin da Ya fi Daɗewa a Sarauta a Arewa Ya Rasu, Bola Tinubu Ya Tura Saƙon Ta'aziyya

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura sakon jaje bayan mutuwar sarkin da ya fi daɗewa a kan karaga a Arewacin Najeriya
  • Bola Tinubu ya ce yana yiwa dukkan mutanen masarautar Asholyio da ma daukacin al'ummar kudancin Kaduna jaje kan rashin
  • Har ila yau, shugaban kasar ya bayyana irin ayyukan cigaba da sarkin ya kawo a jihar Kaduna musamman a bangaren ilimin zamani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Shugaban kasa Bola Tinubu ya tura sakon jaje bayan mutuwar sarkin Moroa, Dakta Tagwai Sambo.

Bola Tinubu ya ce marigayin ya cancanci a yaba masa bisa ayyukan cigaba da ya kawo a lokacin rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Ana cikin talauci, Tinubu ya fadi hanyar da za ta zamo mafita ga 'yan Najeriya

Dakta Tagwai Sambo
Sarkin mafi dadewa kan mulki ya rasu. Hoto: King Carbon D-mash Yamyjack
Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da mai taimakawa Bola Tinubu a harakokin sadarwa, Ajuri Ngelale ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki mafi daɗewa kan karaga

A cikin sakon da Ajuri Ngelale ya wallafa ya nuna cewa mai martaba Dakta Tagwai Sambo ya shafe shekaru 58 a kan karaga.

Hakan ya sanya shi zama basaraken da ya fi kowane sarki tsawon rai a kan karagar mulki a Arewacin Najeriya.

Saƙon ta'aziyyar shugaba Bola Tinubu

Biyo bayan rasuwar sarkin, shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sakon ta'aziyya da dukkan iyalansa, masarautar Moroa da daukacin mutanen Kaduna.

Shugaba Tinubu ya ce sarkin ya kasance gwarzo a kan samar da zaman lafiya da cigaban al'umma.

Cigaban da Sarki Tagwai Sambo ya kawo

Bola Tinubu ya bayyana cewa lallai an yi rashin jagora wanda ya bada gudunmawa sosai a ɓangaren ilimi.

Kara karanta wannan

'Kar ka fara da bada hakuri': 'Yan kasa sun yi martani ga Tinubu, sun fadi mafita ga Najeriya

Shugaba Tinubu ya ce Dakta Tagwai Sambo ne ya jagoranci kafa jami'ar jihar Kaduna kuma shi ya zamo shugabanta na farko a tarihi.

Sarki Sanusi II ya yi maganar tsarin mulki

A wani rahoton, kun ji cewa Muhammadu Sanusi II ya magantu kan halin da Najeriya ke ciki da ma kokarin komawa tafarkin mulkin firaminista.

Sarki Sanusi II yana ganin sauya tsarin mulki ba shi ne zai magance matsalolin da su ka dabaibaye Najeriya a halin da ake ciki ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng