An Zaɓi Dalibai Domin Samun Lamunin Karatun NELFUND, Gwamnati Ta Bayyana Adadinsu

An Zaɓi Dalibai Domin Samun Lamunin Karatun NELFUND, Gwamnati Ta Bayyana Adadinsu

  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana adadin daliban da gwamnati ta zaɓa domin samun lamunin karatu
  • Sanata Godswill Akpabio ya ce daliban sune karon farko da za su fara cin gajiyar shirin da shugaba Bola Tinubu ya kawo na NELFUND a Najeriya
  • Wani dalibi a jami'ar tarayya da ke Kashere, Ibrahim Mahadi ya bayyana yadda karfin gwiwarsa ya ragu da ya ji dalibai 30,000 kawai aka zaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi albishir ga daliban da suka nemi lamunin karatun NELFUND.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa a halin yanzu an kammala zaɓen daliban da za suci moriyar shirin a karon farko.

Kara karanta wannan

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, ya nemi ayi sulhu da gwamnati

Bola Tinubu
Sanata Akpabio ya bayyana adadin daliban da za a ba lamunin NELFUND. Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Sanata Godswill Akpabio ya bayyana haka ne a jiya Talata, 18 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NELFUND: Adadin daliban da ka zaɓa

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa an zaɓi dalibai sama da 30,000 cikin dinbin dalibai da suka nemi lamunin NELFUND.

Sanata Godswill Akpabio ya ce samar da lamunin yana daga cikin abin da yake faranta masa rai kasancewar an kawo shi ne a karkashin jagorancinsa a majalisa.

Amfanin lamunin NELFUND ga karatun dalibai

Sanata Godswill Akpabio ya ce bayar da lamunin NELFUND zai taimaka matuka ga talakawa wajen samun damar zurfafa karatu, rahoton Nairametrics.

Sanatan ya ce saboda ba 'yan kasa damar karatu ba tare da bambanci ba ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙirƙiro shirin.

Amfanin canza taken Najeriya

Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa canza taken Najeriya da aka yi yana da muhimmanci sosai ga zaman lafiya.

Kara karanta wannan

PDP ta tsoma baki kan rikicin Ribas, yayin da APC ke neman a sanya dokar ta baci

Akpabio ya ce da tun farko an canza taken da ya sanyawa yan kasa kishi ta yadda ba za a samu masu ayyukan ta'addanci da garkuwa da mutane ba.

Legit ta tattauna da dalibin jami'a

Wani dalibin jami'ar tarayya da ke Kashere a jihar Gombe, Ibrahim Mahadi ya ce zaben dalibai 30,000 ba zai tabuka komai ba wajen sharewa dalibai hawaye.

Ibrahim Mahadi ya ce matukar zaben wanda za a ba lamunin za a yi to ba lallai wanda ba su da uwa a gindin murhu su samu ba kuma hakan barazana ne ga karatun dalibai.

Dalibin ya yi kira ga gwamnatin tarayya kan ta bada lamunin ga dukkan daliban da suka nema matukar ana nufin ganin 'ya'yan talakawa sun yi karatu ne.

Iyaye sun koka kan lamunin NELFUND

A wani rahoton, kun ji cewa iyaye da ɗalibai sun koka a kan kwaskwarimar da gwamnatin tarayya ta yi wa sabon tsarin ba da lamuni ga dalibai.

Kara karanta wannan

Badaƙalar Emefiele: An gano yadda mutane 4 suka kasafta $6.2m da aka sata daga CBN

Shugaban kungiyar daliban jami'a ta kasa (NAUS), kwamared Obaji Marshall, ne ya magantu a kan canje-canje da gwamnati ta yi a cikin shekarar 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng