"Ana Kokarin Kawo Mana Boko Haram," Kwankwaso Ya Faɗi Masu Shirin Hargitsa Kano

"Ana Kokarin Kawo Mana Boko Haram," Kwankwaso Ya Faɗi Masu Shirin Hargitsa Kano

  • Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya na koƙarin tayar da yamutsi a jihar Kano domim cimma wata manufa
  • Jagoran Kwankwasiyya ya bayyana yaƙinin cewa mutanen Kano ba zasu bari wani ya wargaza masu zaman lafiya ba
  • Kwankwaso ya faɗi waɗannan kalamai ne yayin da yake martani kan abubuwan da ke faruwa a jihar tun bayan mayar da Sarki Sanusi II

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Jagoran jam'iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, ya ɗora laifin duk rikicin da ke faruwa a jihar Kano kan gwamnatin tarayya.

Kwankwaso ya yi zargin cewa gwamnatin ta APC na ƙoƙarin kawo ƴan tada kayar baya masu kama da Boko Haram a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu na shirin sanya dokar ta baci a Kano domin kwace mulki? Gaskiya ta fito

Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya da kokarin kawo yan tada kayar baya a Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake martani kan abubuwan da ke faruwa na rikicin sarauta, inda jami'an tsaro ke goyon bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton Vanguard, tsohon gwamnan ya ce mutanen Kano ba za su bari wasu su zo su kawo cikas ga gwamnatin da suka zaɓa da hannayensu ba.

Kwankwaso na zargin Gwamnatin Tinubu

Da yake jawabi a wurin kaddamar da ginin titunan karkara mai tsawon kilomita 82 a mahaifarsa Madobi, jagoran Kwankwasiyya ya ce:

"Muna da mabiya da yawa saboda mutane sun yarda da mu, mu ma mun yarda da su kuma gwamnatinmu ta NNPP ta kuduri aniyar yi musu aiki a duk inda suka zabe ta.
“Ba za mu nade hannayenmu muna kallon makiyan jihar suna wargaza zaman lafiya a jiharmu ba, za mu yi duk mai yiwuwa don marawa gwamna baya.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Kwankwaso ya tona asirin masu zuga Aminu Ado, ya fadi shirinsu

"Akwai wasu ƴan Kano, makiyan jihar, waɗanda ke fama da taɓin hankali, suke zuga gwamnatin tarayya ta kwace Kano ta hanyar ayyana dokar ta ɓaci."

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya tana sauraron wasu gurbatattun ƴan siyasa daga Kano, waɗanda ba za su iya komai ba sai dai su kaita su baro, Leadership ta rahoto.

Kwankwaso ya ba Gwamna Abba shawara

A wani rahoton kuma Rabiu Kwankwaso ya bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf shawara kan ɓangaren da ya kamata gwamnatinsa ta fi mayar da hankali.

Jagoran Kwankwasiyya ya bayar da shawarin ne yayin da gwamnan da muƙarrabansa suka kai masa ziyarar barka da Sallah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262