Kwankwaso Ya Shiga Babbar Matsala, Jam’iyyar APC Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Kama Shi

Kwankwaso Ya Shiga Babbar Matsala, Jam’iyyar APC Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Kama Shi

  • Jam’iyyar APC ta nemi jami'an tsaro a Najeriya da su gaggauta cafke tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso
  • Shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya zargi Rabiu Kwankwaso da furta kalaman kazafi ga gwamnatin tarayya
  • An ji Kwankwaso yana cewa gwamnatin tarayya karkashin jam'iyyar APC tana kokarin kawo cikas ga zaman lafiyar Kano

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta cafke Rabiu Kwankwaso, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP.

An ruwaito cewa Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC da kyankyasar sababbin ‘yan ta’adda a Kano.

Kara karanta wannan

Rikicin masarauta: Kwankwaso ya bayyana masu son kawo hargitsi a Kano

APC ta yi magana kan zargin da Kwankwaso ya yi wa gwamnatin tarayya
APC ta bukaci jami’an tsaro su gaggauta kama Kwankwaso. Hoto: @KwankwasoRM, @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Dalilin APC na neman a kama Kwankwaso

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya nemi a kama Kwankwaso a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 18 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani bangare na sanarwar da Alhaji Abbas ya fitar na cewa:

“Akwai bukatar jami’an tsaron Najeriya su gaggauta kama Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, su kuma tilasta shi ya bayyana sunayen wadanda ke daukar nauyin 'yan ta'adda a jihar.”

"Kwankwaso na son ayi rigima a Kano" - APC

An ce tsohon gwamnan na Kano ya yi wannan ikirarin ne a ranar Litinin, wajen bikin kaddamar da aikin gina titin karkara mai tsawon kilomita 85 a mahaifarsa Madobi.

Da yake martani kan wannan zargi, Alhaji Abbas ya roki jami'an tsaro da su tsare Kwankwaso har sai ya fadi sunayen masu daukar nauyin ta'addanci a jihar, in ji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

"Ana kokarin kawo mana Boko Haram," Kwankwaso ya faɗi masu shirin hargitsa Kano

Shugaban ya yi nuni da cewa wadannan kalamai na nuni ne da wata muguwar manufa da Kwankwaso da makarrabansa suke da ita na kawo tashin hankali a Kano.

"Gwamnati ke kyankyasar 'yan ta'adda" - Kwankwaso

Tun da fari, mun ruwaito cewa Kwankwaso ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Tinubu na kyankyasar wasu sababbin nau’in ‘yan ta’adda a Kano.

Kwankwaso ya yi zargin ne saboda yadda aka jibge jami’an tsaro a karamar hukumar Nasarawa inda Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ke gudanar da sarautarsa a yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.