‘Kar Ka Fara da Bada Hakuri’: ’Yan Kasa Sun Yi Martani ga Tinubu, Sun Fadi Mafita Ga Najeriya

‘Kar Ka Fara da Bada Hakuri’: ’Yan Kasa Sun Yi Martani ga Tinubu, Sun Fadi Mafita Ga Najeriya

  • Maganar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar sallah na bukatar 'yan Najeriya su kara juriya ta tayar da ƙura
  • Shugaban kasar ya yi kira ga 'yan Najeriya ne da su cigaba da hakuri da juriya kan wahalhalun da ake ciki domin gina kasa
  • Legit ta tattauna da Haruna Abdullahi domin jin yadda zai kalli maganganun da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi da martanin da aka masa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Saƙon da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura a ranar sallah ya sha suka daga 'yan Najeriya.

A cikin sakon, shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa a halin yanzu, ana bukatar 'yan Najeriya da su kara juriya da sadaukarwa domin ci gaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Sarkin da ya fi daɗewa a sarauta a Arewa ya rasu, Bola Tinubu ya tura saƙon ta'aziyya

Shugaba Tinubu
Yan Najeriya sun yi martani ga kalaman Bola Tinubu kan kara hakuri. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattauna da 'yan Najeriya inda suka bayyana abin da yafi dacewa gwamnati ta yi domin samar da mafita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sai Gwamnatin Tinubu ta fara cika alkawura"

Wani malami a Jami'ar Sa'adatu Rimi, Dakta Abdussalam Kani ya ce akwai bukatar gwamnati ta fara cika alkawuran da ta yi idan ana son kawo cigaba a kasa.

Malamin ya ce gwamnati ta yi alkawarin gyara matatar mai a Fatakwal amma shiru har yanzu sai kuma suka fito da maganar sayen sabon jirgi ga shugaban kasa wanda hakan ba hanyar cigaba bane.

"Da na gaba ake gane zurfin ruwa"

Sakataren kungiyar kimiyyar siyasa ta kasa (NPSA) Dakta Bakare Adegbola ya ce yan siyasa ne ya kamata su fara nuna sadaukarwa kafin yin kira ga talakawa.

Ya ce matuƙar 'yan siyasa za su cigaba da rayuwar ƙasaita da busha-sha to ba yadda za a yi ace talakawa su nuna sadaukarwa.

Kara karanta wannan

"Ba a nan kawai ake wahala ba," Shugaba Tinubu ya gargadi jama'an Najeriya

"Shugabanni su ji tsoron Allah"

Wani malamin makaranta, Umar Tijjani ya ce ya kamata shugabannin Najeriya su ji tsoron Allah wajen samar da mafita ga kasa.

Ya ce yadda abubuwa suka yi tsada kamata ya yi su fara neman mafita ba wai kira ga talakawa kan sadaukarwa ba.

Legit ta tattauna da Haruna Abdullahi

A cikin hirar da Legit ta yi da Haruna Abdullahi ya tabbatar da cewa akwai bukatar shugaban kasar ya fara aiki da abin da yake fada.

Haruna Abdullahi ya ce an dade ana kira ga yan Najeriya kan su kara hakuri da juriya amma ba su ga fa'idar hakan ba, kuma shugabannin ba sa nuna hakan a zahiri.

Ana kashewa dalibai N4bn a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana yadda ta ke kashe mukudan kudi domin ciyar da ɗalibai da suke wasu makarantu a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Ana cikin talauci, Tinubu ya fadi hanyar da za ta zamo mafita ga 'yan Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa mai taimakawa Uba Sani kan ciyar da ɗalibai a makarantu, Dakta Fauziyya Ado ce ta fitar da rahoton ga manema labarai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng