Ana Gobe Sallah, Bola Tinubu Ya Tura Sako na Musamman ga ’Yan Najeriya

Ana Gobe Sallah, Bola Tinubu Ya Tura Sako na Musamman ga ’Yan Najeriya

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura sako na musamman ga yan Najeriya yayin da ake shirin sallar layya a gobe Lahadi
  • A cikin sakon, Bola Tinubu ya bayyana yadda Musulmi za su yi amfani da bikin babbar sallah wajen kawo cigaba ga Najeriya
  • Mai taimakawa Bola Tinubu kan harkokin sadarwa, Ajuri Ngelale ne bayyana haka cikin wani sako a yau Asabar, 15 ga watan Yuni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura sako na musamman yayin da al'ummar Musulmi ke shirin fara hidimar babbar sallah.

Bola Tinubu ya yi kira na musamman ga Musulmi kan sadaukarwa domin kowo nasara da cigaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bukaci daraktan hukuma dan Arewa da Buhari ya nada ya yi murabus

Shugaba Tinubu
Tinubu ya yi kira na musamman kan hidimar sallah. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Legit ta samu sanarwar ne a cikin wani sako da jami'in yada labaran fadar shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya buƙaci a nuna sadaukarwa

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi nuni da cewa babbar sallah tana da alaƙa da sadaukarwa ne da aka yi a baya.

Saboda haka ya buƙaci yan Najeriya da su nuna sadaukarwa domin ta hanyar haka ne kawai za a gina kasa mai inganci.

Haka zalika Tinubu ya mika godiya kan sadaukarwa da juriya da yan kasa suka nuna cikin shekara daya da ya yi yana gyaran Najeriya.

Tinubu ya ce Najeriya na bukatar addu'a

Bola Tinubu ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su yi kokarin yin adduo'i na musamman ga kasar a wannan lokaci mai albarka.

Shugaban kasar ya ce a hakikanin gaskiya Najeriya na buƙatar adduo'i domin samun zaman lafiya da cigaba.

Kara karanta wannan

Kungiyar CODE ta fadi mataki 1 da Tinubu zai dauka domin magance matsalar tsaro

Tinubu: 'Ba zan ba ku kunya ba'

Dangane da halin da ake ciki na matsin rayuwa, Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ta fara daukan saiti kuma ana daf da cin nasara.

Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ba zai ba yan Najeriya kunya ba domin yana kokarin tabbatar da ya cika alkawuran da ya yi.

An ba Bola Tinubu shawari kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa wata Kungiya mai zaman kanta (CODE) ta yi kira na musamman ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan magance matsalolin tsaron Nijeriya.

Kungiyar ta ce bayan cika shekaru 25 ana mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya ya kamata a samu cigaba wajen magance matsalolin tsaron kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng