Hajj 2024: Adadin Alhazan da Suka Rasu a Saudiya Ya Kai 19, Wasu 17 Sun Bace

Hajj 2024: Adadin Alhazan da Suka Rasu a Saudiya Ya Kai 19, Wasu 17 Sun Bace

  • Kasashen Jordan da Iran sun ruwaito cewa akalla mahajjata 19 daga kasashensu ne suka rasu a yayin aikin hajjin bana
  • A ranar 16 ga Yuni, ma'aikatar harkokin wajen Jordan ta sanar da cewa alhazanta 14 ne suka mutu, yayin da wasu 17 suka bace
  • A gefe guda kuma hukumar agaji ta Red Crescent ta Iran, ta bayyana cewa zuwa yanzu mahajjatan Iran biyar suka rasu a Saudiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Makkah, Saudiya - Hukumomin kasashen Jordan da Iran sun bayar da rahoton cewa, akalla mahajjata 19 daga kasashensu ne suka mutu a lokacin aikin hajji a kasar Saudiyya sakamakon tsananin zafin rana.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Jordan ta sanar da cewa "Alhazan Jordan 14 ne suka mutu yayin da wasu 17 suka bace" yayin da suke gudanar da aikin Hajji.

Kara karanta wannan

Musulmi na murnar Sallah, mazauna Kano na bakin cikin kwace gonakinsu

Tsanani zafi ya yi ajalin mutane 19 a aikin Hajjin 2024 a Saudiya.
Saudiya: Alhazai 19 sun rasu a wajen aikin Hajji,wasu 17 sun bace
Asali: Getty Images

Daga baya ma’aikatar ta tabbatar da cewa mahajjatanta 14 sun mutu sakamakon “buguwar rana saboda tsananin zafi,” kamar yadda jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton Iran kan mutuwar mutane 5

A daya bangaren, shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent na Iran, Pirhossein Koolivand, ya bayar da rahoton cewa:

"Alhazan Iran biyar ne suka rasa rayukansu a Makka da Madina a lokacin aikin hajjin bana."

Aikin Hajji na daya daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar. Yana zama wajibi ga dukkanin musulmin da ke da ikon gudanar da shi akalla sau daya a rayuwarsu.

Kalubalen zafin rana a Hajjin bana

Rahoton BBC ya nuna cewa a bana, yanayin zafi a lokacin aikin Hajji ya haura ma'aunin Celsius 40, wanda ya yi tasiri a kan kusan Musulmi miliyan 1.8 da ke aikin Hajjin.

A makon da ya gabata, shugaban cibiyar nazarin yanayi ta Saudiya, Ayman Ghulam, ya yi gargadi cewa:

Kara karanta wannan

Aiki da cikawa: Ana tsaka da bikin babbar sallah, sojoji sun kashe dan bindigan da ya addabi Kaduna

“Za a samu karuwar yanayin zafi daga digiri 1.5 zuwa 2 (Celsius) a aikin Hajjin bana, zafin da ya haura yadda aka saba gani a Makka da Madina."

Jarumar Nollywood, Stella ta mutu

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitacciyar jarumar fina-finan Kudancin Najeriya, Stella Ikwuegbu, ta mutu a ranar Lahadi, 16 ga watan Yunin 2024.

Stella Ikwuegbu wanda ta shiga harkar fim ne a shekarar 1990 ta fito a fina-finan da suka hada da Ukwa, Spoiler da Madam Koikoi, ta mutu bayan fama da jinya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel