Karanta wasu bayanai 8 masu muhimmanci game da aikin Hajji da Ka’aba

Karanta wasu bayanai 8 masu muhimmanci game da aikin Hajji da Ka’aba

A yayin da alhazai ke shirin fara gudanar da aikin Hajji a kasar Saudiyya, hukumar dake kula da alhazan Najeriya, NAHCON, ta bayyana wasu muhimman bayanai guda 8 game da aikin Hajji da dakin Allah, Ka’abah don amfanin mahajjata.

Legit.ng ta ruwaito NAHCON ta bayyana haka ne a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda ta lisaffa wadannan muhimman bayanai kamar haka:

KU KARANTA: An zabi Shehin Malamin Najeriya don gabatar da tunatarwa cikin harshen Hausa a Masallacin Madina

1- Annabi Adam ne ya fara gina Ka’aba dakin Allah

2- Sau daya Annabi ya taba gudanar da aikin Hajji a rayuwarsa

3- Kakan Annabi Muhammadu, Abdul-Muttalib ne ya sake gano inda rijiyar Zamzam take

4- Ziyarar Madina bata cikin farillan Hajji

5- An wajabta ma Maza da Mata sanya Ihrami a yayin aikin Hajji

6- Hateem (Hijr Ismail) na daga cikin wani yanki na Ka’aba

7- An bukaci Maza su bayyana kafadarsu ta dama a waje yayin gudanar da Dawafi

8- A shekara ta 9 bayan Hijira ne Allah Ya wajabta aikin Hajji

A wani labarin kuma, hukumar alhazan Najeriya ta kammala jigilar mahajjatan Najeriya da suka kai 44,450 zuwa kasar Saudiyya daga jahohin 36 da babban birnin tarayya Abuja domin gudanar da aikin Hajji. Sai dai wannan adadi bai hada har da mahajjatan jirgin yawo ba.

A ranar Litinin, 5 ga watan Agusta ne jirgin karshe ya tashi daga babban birnin tarayya Abuja dauke da maniyyata 301 daga jahohin Abuja, Sakkwato, Abia, Enugu, Ebonyi, Delta, Cross Rivers, Delta, Zamfara, Kaduna da Anambra da jami’an hukumar alhazai guda 19, inda ya tashi da misalin karfe 8:53 na dare.

Gwamnatin kasar Saudiyya ta baiwa gwamnatin Najeriya kujeru 95,000, inda gwamnatocin jahohi suka samu kujeru 65,000 yayin da kamfanonin jiragen yawo suka samu kujeru 30,000.

Zuwa ranar Litinin an samu alhazai 1,687,226 daga dukkanin sassan duniya sun isa kasar Saudiyya ta ruwa, ta jirgin sama da kuma ta kasa don gudanar da aikin Hajji a kasar Saudiyya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel