Tinubu: Fadar Shugaban Kasa ta Fadi Wadanda Suka Jefa Najeriya a Halin Ha'ula'i

Tinubu: Fadar Shugaban Kasa ta Fadi Wadanda Suka Jefa Najeriya a Halin Ha'ula'i

  • Gwamnatin tarayya ta yi martani ga labarin da wata jarida a kasar waje ta wallafa na cewa kasar nan na fuskantar mafi munin tabarbarwar tattalin arziki a tarihinta
  • Hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kafafen yada labarai, Bayo Onanuga ya dora laifin matsalolin da ake fuskanta kan gwamnatocin baya da gwamnatinsu ta gada
  • Ya ce kamata ya yi jaridar ta waiwayi yadda gwamnatin Najeriya ke kokarin magance matsalolin hauhawar farashi ta hanyar habaka noma da sauran tsare-tsare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Gwamnatin tarayya ta wanke kanta daga wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fama da su, tare da bayyana wadanda ta ke zargi da laifin rugurguza tattalin arzikin kasa.

Kara karanta wannan

Rayuwar Tinubu za ta iya shiga hadari, majalisa ta nemi a siya masa sabon jirgi

Mashawarcin shugaba Bola Tinubu na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne a martaninsa ga labarin da New York Times ta wallafa ya ce gwamnatocin baya ne ke da alhakin tabarbarewar tattalin arziki.

Bola Tinubu
Fadar shugaban kasa ta ce matsin tattalin arzikin Najeriya laifin Jonathan, Tinubu da Buhari ne Hoto: Ajuri Ngalale
Asali: Twitter

Premium Times ta wallafa cewa jaridar New York Times ta wallafa wani labari da ke bayyana cewa Najeriya na fuskantar mafi tsananin lalacewar tattalin arziki a lokacin Bola Ahmed Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ana wallafa mugayen labarai kan Afrika,” Onanuga

Hadimin shugaban kasa na musamman kan yada labaran, Bayo Onanuga ya yi martani ga labarin da Ruth Maclean and Ismail Auwal su ka wallafa a jaridar New York Times su na fadan yadda gwamnatin Tinubu ta zo da matsi mafi tsanani a Najeriya.

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Onanuga na ganin wannan wani abu ne da jaridun kasashen waje su ka saba na wallafa labarai marasa kyau kan nahiyar Afrika.

Kara karanta wannan

NELFUND ta fadi daliban da su ka cancanci lamunin karatu

A ganinsa, kyautuwa ya yi jaridar ta karkatar da akalarta wajen bankado ayyukan ci gaba da kokarin gyara tattalin arzikin Najeriya da gwamnatin Tinubu ke yi.

Gwamnatin Tinubu ta kawo mafita

Onanuga ya ce duk da kokarin da gwamnatinsu ta ke yi, sun gaji matsalolin tattalin arziki da suka samo asali daga kudirorin gwamnatocin baya kamar biyan tallafin man fetur da karbo dimbin basussuka.

Hadimin shugaban ya ce amma su na kokarin gyara halin da ake ciki ta hanyar bunkasa noma da wadata kasa da abinci domin dakile hauhawar farashi.

Ana da labari cewa rahoton da aka samu daga babban mai binciken kudi ya nuna yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta bar Najeriya da bashi.

An yi zanga-zanga kan mulkin Tinubu

A wani labarin kun ji cewa wani makusancin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Kassim Balarabe Musa ya jagoranci dandazon matasa zanga-zanga a jihar Kaduna saboda matsin rayuwa.

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Matasan sun yi zanga-zngar a ranar 12 Yuni, 2024 su na neman shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauka daga mulkin Najeriya saboda mawuyacin halin da ake ciki a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel