Sanusi II Ya Yi Hawa: ’Yan Sanda Sun Yi Magana Kan Yadda Aka Yi Sallar Idi a Kano

Sanusi II Ya Yi Hawa: ’Yan Sanda Sun Yi Magana Kan Yadda Aka Yi Sallar Idi a Kano

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano sun ce sun gamsu da yadda aka gudanar da Sallar Idi a yau Litinin a kananan hukumomi 44 na jihar
  • A zantawar Legit Hausa da wasu mazauna jihar, sun yi tsokaci kan yadda aka gudanar da Sallar da kuma gamsuwa da matakan tsaro
  • Wannan dai na zuwa ne bayan da Sarki Muhammadu Sanusi ya yi hawan Sallah kamar yadda aka saba, amma cikin sabon salo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta nuna gamsuwarta kan yadda aka gudanar da Sallar Idi a fadin jihar cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin hankula ba.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: An bayyana jihar da Shugaba Tinubu zai yanka ragon layyarsa

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Usaini Gumel ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) cewa ya ji dadin yadda mutanen Kano suka gudanar da Sallar cikin tsanaki.

'Yan sanda sun yi magana kan yadda aka yi Sallar Idi a Kano
AIG Gume ya nuna gamsuwa kan yadda aka yi Sallar Idi a Kano.
Asali: Facebook

CP Gumel wanda jaridar Daily Nigerian ta ce an ƙara masa matsayi zuwa mataimakin Sufeta-Jana (AIG) ya jinjinawa mutanen Kano kan dattakon da suka nuna a yau Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar AIG Usaini Gumel:

"Rahotanni daga kananan hukumomi 44 na jihar Kano sun nuna cewa an gudana da Sallar Idi cikin kwanciyar hankali, babu barazana ga rayuka ko dukiyar al'umma."

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an tashi da fargabar za a yi tashin hankali a jihar saboda rigimar masarautar Kano tsakanin magoya bayan Sarki Sanusi II da Ado Bayero.

Sanusi II; Batu kan rigimar masarautar Kano

Rigimar masarautar ta fara ne tun bayan da Gwamna Abba Yusuf ya rusa masarautun jihar biyar da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkira.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: NDLEA ta kama miyagun kwayoyin da aka shirya harkallarsu a sallah a Kano

Haka zalika, dawo da Muhammadu Sanusi II a kan karagar mulkin jihar ya kara jawo rigimar ta yi tsamari, lamarin da ya jawo zanga-zanga da zuwa kotu.

Domin kare fada tsakanin magoya bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero da Sarki Sanusi II, a ranar Juma'a, AIG Usaini Gumel ya sanar da haramta hawan Daba a fadin Kano.

Legit Hausa ta yi ra'ayin mutanen Kano

A zantawar Legit Hausa da wasu mazauna Kano kan yadda aka gudanar da Sallar Idin na yau, su ma sun bayyana gamsuwa da zaman lafiyar da aka samu.

Abba Hassan Gazawa, daga karamar hukumar Gezawa ya ce sun gudanar da Sallar Idi lami lafiya, kuma rigimar masarautar ba ta shafi yankin nasu sosai ba tunda suna wajen gari.

Isma'il ATO, daga karamar hukumar Kano ta tsakiya, ya nuna cewa an yi Sallah lafiya, amma dai wasu sun so tayar da tarzoma, aka dakile su.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: 'Yan sanda sun dauki mataki kan hawan Sallah a Kano

Isma'il, ya ce jami'an tsaro sun tsaurara matakan tsaro a lunguna da sakon birnin jihar, lamarin da ya ce ya taimaka wajen hana bata gari aikata abin da zai kawo rashin zaman lafiya.

Hafsat Sani, wadda ta nemi a sakaya inda take zama, ta nuna jin dadin yadda aka gudanar da Sallar bana, tana mai cewa zaman Sarki Sanusi II a fadar jihar ya sa Sallar ta yi armashi.

Hafsat Sani ta yi kira ga daukacin al'ummar jihar Kano da su ajiye bambancin akidar masarauta, su rungumi zaman lafiya da kuma sada zumunci a wannan lokaci na bikin Sallah babba.

Kano: Sarki Sanusi II ya yi hawan Sallah

Tun da fari, mun ruwaito cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi biris da umarnin 'yan sanda, ya gudanar da hawan Sallah kamar yadda aka saba.

Mai martaba Sanusi II ya gudanar da hawan ne bayan ya jagoranci Sallar Idi a masallacin Kofar Mata da ke cikin kwaryar Kanon Dabo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel