Gwamna Ya Cigaba da Tonon Silili, Ya Fallasa Masu Sakin ‘Yan Bindigan da Aka Kama

Gwamna Ya Cigaba da Tonon Silili, Ya Fallasa Masu Sakin ‘Yan Bindigan da Aka Kama

  • Mai girma Dauda Lawal Dare ya ce sai an yi nasarar cafke wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne, sai a ji an fito da su a kotu
  • Gwamnan jihar Zamfara yana zargin akwai wasu manyan mutane masu wuka a gindin murhu da ke kawo masa matsala
  • Gwamna Dauda ya ce wadannan mala’u da ke Abuja, su na da alaka da ‘yan bindigan da suka hana Zamfara zaman lafiya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Zamfara - Har yanzu ana cigaba da fama da matsalar ‘yan bindiga a Arewa maso yamma, lamarin ya yi kamari a jihar Zamfara.

Mai girma gwamnan Zamfara ya koka kan yadda aka gagara shawo kan matsalar, Dauda Lawal Dare ya ce abin ya fi karfinsa.

Kara karanta wannan

A karon farko, Sanusi II yayi maganar rikicin sarautar Kano da Aminu Ado Bayero

Gwamna Dauda Lawal
Gwamnan Zamfara ya koka kan matsalar sakin 'yan bindiga Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Gwamnan Zamfara ya ce ana sakin 'yan bindiga

A wani bidiyo da tashar AIT ta daura, an ji gwamnan na jihar Zamfara yana zargin kotu da sakin mutanen da ake zargi da laifi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dauda Lawal Dare ya ce ana kama mutane kuma har su amsa laifuffukansu, amma daga baya sai alkalai su ba da belinsu a kotu.

Gwamnan ya ce wadanda aka kama dumu-dumu da makamai sun kashe bayin Allah, suna samun ‘yanci idan an je gaban alkali.

'Yan bindiga: Gwamna ya zargi manyan Abuja

Dauda Lawal ya yi ikirarin wasu manyan mutane daga birnin tarayya Abuja suna da hannu wajen sakin wadanda ake zargi da laifi.

Manyan mutanen suna magana da jagororin ‘yan bindigan kuma a karshe suyi masu hanyar da za su tsere daga hannun hukuma.

Kara karanta wannan

Kotu ta daure matashin da ya sace dabbobi, ya kalmashe kudin mutane a aljihu

Daily Post ta ce jawabin gwamnan ya zo ne a lokacin da ake rantsar da sababbin alkalan kotun majistare da aka yi a garin Gusau.

Gwamna ya bar 'yan bindiga da Allah?

Gwamnan ya yi Allah ya isa a madadin al’ummar jihar Zamfara a kan wannan abin da yake faruwa ganin irin barnar da ake yi.

Dauda Lawal ya ce akwai ‘dan bindigan da aka gano a Bauci, aka cafko shi kuma aka yi nasarar gurfanar da shi a kotu a birnin Gusau.

Wani lokaci wadanda aka kama za su amsa laifin da suka aikata, bayan wani lokaci sai a ji cewa alkali ya ba da belinsu, an fito da su.

Gwamna Dauda da rashin tsaron Zamfara

A baya an rahoto Gwamna Dauda Lawal ya na magana kan halin rashin tsaro a Zamfara shekara guda bayan ya dare kan mulki.

Dauda ya yi nuni da cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu bai san halin da ake ciki ba, ya kuma ce za a iya magance matsalar cikin kwanaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel