"Ba Ku Isa Ba": Gwamnoni Sun Shiga Uku, Majalisa Za Ta Yi Doka Kan Mafi Karancin Albashi

"Ba Ku Isa Ba": Gwamnoni Sun Shiga Uku, Majalisa Za Ta Yi Doka Kan Mafi Karancin Albashi

  • Yayin da ake ci gaba da tababa kan mafi karancin albashi, Majalisar Tarayya za ta samar da doka mai tsauri kan lamarin
  • Majalisar ta tabbatar da shirinta na samar da dokar da za ta tilasta gwamnoni 36 a Najeriya biyan mafi karancin albashi
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin hulda da jama'a na Majalisar, Yemi Adaramodu ya fitar a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Tarayya ta tabbatar da shirin gabatar da kudiri da zai tilasta gwamnoni biyan mafi karancin albashi.

Shugaban kwamitin hulda da jama'a na Majalisar, Sanata Yemi Adaramodu shi ya tabbatar da haka a yau Juma'a 14 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya za su tafi maƙwabciyarta domin wanzar da zaman lafiya, an jero dalilai

Majalisa za ta yi dokar tilasta gwamnoni biyan mafi karancin albashi
Majalisar Tarayyar ta shirya ƙirƙirar doka kan mafi karancin albashi. Hoto: Nigerian Senate.
Asali: Facebook

Ƙarin albashi: Majalisa za ta yi doka

Adaramodu ya ce kudirin zai tilasta gwamnoni biyan mafi karancin albashin da zarar an tsayar da mafita a cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce za a tabbatar da kudirin ya zama doka wanda za ta hukunta duka gwamanonin da suka ki bin tsarim mafi karancin albashi.

Shirin majalisa kan mafi karancin albashi

"Za mu samar da kudiri mai tsauri wanda Shugaba Tinubu zai sanyawa hannu domin bin tsari."
"Idan muna maganar mafi karancin albashi, ba fada ba ne na iya Gwamnatin Tarayya da NLC saboda haka wasu ke ganin abin."
"Za mu samar da doka mai tsauri wanda jihohi ko ma'aikatu masu zaman kansu dole su bi dokar ko su fuskanci hukunci."

- Sanata Yemi Adaramodu

Majalisa ta gargadi gwamnoni kan mafi karancin albashi

Adaramodu ya ce idan har dokar ta tabbata to duka gwamanonin ya zama musu wajibi su biya albashin domin ba fada ne tsakanin NLC da Gwamnatin Tarayya ba.

Kara karanta wannan

"Yadda Tinubu da jihohi za su samu kudin biyan sabon albashin ma'aikata," in ji Falana

Ya kuma ba da tabbacin cewa dokar ba za ta zo da wasa ba saboda tabbatar da mafi karancin albashin ya zama zahiri.

Ma'aikata sun tura sako ga gwamnoni

Kun ji cewa wasu ma'aikata a Najeriya sun bukaci gwamnonin jihohi su rage alawus dinsu domin biyan mafi karancin albashi.

Ma'aikatan sun bayyana haka yayin da kungiyar gwamnonin ta ce ba za ta iya biyan mafi karancin albashin N70,000 ba a halin da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.