Sarkin Kano Sanusi II Ya Yi Magana Yayin da Aka Yanke Hukunci a Shari'ar Aminu Ado

Sarkin Kano Sanusi II Ya Yi Magana Yayin da Aka Yanke Hukunci a Shari'ar Aminu Ado

  • A karon farko tun bayan nada shi sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi ya magantu kan halin da Najeriya ke ciki da ma kokarin komawa tafarkin mulkin firaminista
  • Sarki Sanusi II yana ganin sauya tsarin mulki ba shi ne zai magance matsalolin da su ka dabaibaye Najeriya a halin da ake ciki ba, inda ya ce ko a da an yi tsarin firaministan
  • Haka kuma Sarkin ya ga rashin dacewar katsalandan da gwamnatin tarayya ke yi cikin mulkin jihohin kasar nan, musamman kan batun masarautun gargajiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tun bayan nada shi Sarkin Kano na 16, a karon farko Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan halin da kasar nan ke ciki da ma hanyoyin da za a kawo gyara.

Kara karanta wannan

Kotu ta daure matashin da ya sace dabbobi, ya kalmashe kudin mutane a aljihu

Sarkin ya yi magana kan abubuwa da dama kamar tsarin mulki, katsalandan da gwamnatin tarayya ke yi a jihohi da yadda za a magance matsalolin.

.

Sanusi
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan halin da Najeriya ke ciki Hoto: Sanusi Lamido Sanusi
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani labari da ya kebanta da Vanguard News, sarki Sanusi ya lissafa wasu abubuwa da ya ke ganin aiwatar da sub a zai haifar da da mai ido ga Najeriya ba

Sanusi II ya yi magana kan tsarin mulki

A makon da ya gabata, ‘yan majalisun kasar nan sun fitar da kudurin da zai ba Najeriya damar komawa kan tsarin mulkin firaminista maimakon wanda ta ke kai na shugaba mai cikakken iko.

Ga jerin wasu daga batutuwan da Sarki Sanusi II ya tabo da yadda za su shafi kasar nan;

1. Tsarin mulkin firaminista

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa komawa tsarin mulkin firaminista ba zai maganta matsalolin da shiyyoyin kasar nan ke fama da su ba.

Kara karanta wannan

NELFUND ta fadi daliban da su ka cancanci lamunin karatu

Ya na ganin Najeriya ta yi fadi da yawa, dauke da kabilu daban-daban a kunshe su a tsarin mulkin firaminisya

2. 'Menene amfanin Majalisu biyu?' - Sarki Sanusi

A hirar da ya yi, Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce bai ga muhimmancin samar da majalisun kasa guda biyu ba, kamar yadda ake da majalisar wakilai da ta dattawa a Najeriya.

Haka kuma sarkin ya na ganin babu wani amfani a ce dole sai an nada minista daga dukkanin jihohin Najeriya. A ganinsa irin wadannan na daga matsalolin da ke kawo cikas wajen tafiyar da harkokin jama’a wanda haka ba zai taimakawa mutanen kasar ba.

3. Raba Najeriya zuwa shiyyoyi

Raba kasar nan zuwa shiyyoyi ba shi ne zai dakile matsalar tsaro da sauran matsaloli da jihohin Najeriya ke fama da shi ba a yanzu, a ra’ayin Sarki Muhammadu Sanusi II.

Ya ce kasar nan na da kabilu da dama da ba zai kyautu a matse su cikin shiyya shiyya ba, domin ko a lokacin da ake kan mulkin firaminista, haka aka yi ta kara raba shiyyoyin.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya fadawa Tinubu ido da ido kuskuren da ya yi a hada kan 'yan kasa

Sarkin ya kara da cewa tun a baya, kabilun Najeriya da ke shiyya daya na kashe junansu saboda bambancin kabila ko al’ada, saboda haka ba daidai ba ne a cushe mutane cikin shiyyoyi.

3. Katsalandan a gwamnati

Sarkin Kano na 16 na ganin gwamnatin tarayya (FG) ba ta kyautawa yadda ta ke tsoma baki cikin al’amuran jihohin Najeriya, musamman kan batutuwan da su ka shafi sarautun gargajiya.

Muhammadu Sanusi II na wannan batu ne yayin da ake ta dambarwar masarauta a Kano inda gwamnatin jihar ta yi zargin ofishin ba wa shugaban kasa shawara kan tsaro da hannu a lamarin.

Sanusi II na ganin kamata ya yi kowa ya tsaya a matsayinsa wajen gudanar da mulki kamar yadda tsarin mulkin kasa ya bayar da dama.

A ganinsa, duk da matsalolin da dimukuradiyya ke tattare da si, ya fi tsarin mulkin firaminista.

4. Yadda za a magance matsalolin Najeriya

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Daya daga hanyoyin da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ke ganin za a magance kasar nan shi ne shugabanni su daina son zuciya tare da mutunta dokar da tsarin mulkin kasa ya samar.

Na biyu shi ne su daina cin dunduniyar jama’a ta hanyar amfani da bambamcin kabila ko addini su na rura wutar gaba da kyashi da tsana saboda biyan bukatar kawunansu.

Sarkin Kano ya shawarci iyaye

A baya mun kawo muku labarin cewa sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II ya shawarci iyaye da su sanya idanu kan shige da fice 'ya'yansu da wadanda ke mu'amalantarsu.

Sarkin ya nanata cewa iyaye su na da muhimmiyar rawa da za su taka a rayuwar 'ya'yansu domin su zama mutane na gari a cikin al'uma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel