Bayan Yanke Hukunci Kan Rigimar Sarautar Kano, Kanawa Sun Tarbi Aminu Ado a Faifan Bidiyo

Bayan Yanke Hukunci Kan Rigimar Sarautar Kano, Kanawa Sun Tarbi Aminu Ado a Faifan Bidiyo

  • Ana tsaka da rigimar sarauta, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya samu tarba daga dubban Kanawa
  • Dubban jama'a ne suka tarbe shi yayin da ya ke dawowa daga masallacin Juma'a a yau 14 ga watan Yuni a birnin Kano
  • Wannan na zuwa ne bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yi kan korafin Aminu Ado na tauye masa hakki a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake tsaka da rigimar sarautar Kano, Aminu Ado Bayero ya samu tarba daga dubban Kanawa.

Sarkin Kano na 15 ya samu tarba ne yayin dawowa daga masallacin Juma'a a yau 14 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Kotu ta yi hukunci a shari'ar Aminu Ado Bayero, ta ci Abba tarar N10m

Dubban jama'a sun tarbi Aminu Ado a Kano
Bayan yanke hukunci kan rigimar sarautar Kano, Aminu Ado ya samu tarba daga Kanawa. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Kano: Kanawa sun tarbi Aminu Ado Bayero

An tarbi Sarkin ne a cikin wani faifan bidiyo da Masarautar Kano ta wallafa a shafin X a yau Juma'a 14 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A faifan bidiyon, an gano dubban jama'a suna nuna kauna ga tsohon Sarkin inda suke ihun cewa "sai ka yi".

Kotu ta ci tarar Abba Kabir N10m

Wannan na zuwa ne yayin da aka yanke hukunci kan korafin da Aminu Ado ya shigar bayan tuge shi a sarautar jihar.

Babbar Kotun Tarayya da ke jihar ta ci tarar gwamnan jihar, Abba Kabir N10m kan take hakkin Aminu Ado.

Kotun ta ce umarnin cafke Ado ya saba ka'ida wanda ya tauye masa ƴancinsa na ɗan Adam a Najeriya.

Daga bisani kotun ta ki amincewa da neman tuge Sanusi II daga kujerarsa kamar yadda Aminu Ado ya nemi alfarmar kotun a jihar.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, babbar kotu ta yanke hukunci a shari'ar sarautar Kano

Aminu Ado ya bukaci karin jami'an tsaro

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya rubuta takarda ta musamman ga kwamishinan ƴan sanda a jihar.

Aminu Ado Bayero ya rubuta takardar domin neman gudunmawar tsaro yayin bukukuwan sallah babba da za a yi a jihar.

Hakan ya biyo bayan shirin hawan sallah da Aminu Ado ya yi niyya duk da kasancewar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.