Magana Ta Ƙare, Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci a Shari'ar Sarautar Kano

Magana Ta Ƙare, Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci a Shari'ar Sarautar Kano

  • A ƙarshe babbar kotun tarayya ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron ƙorafin da ya shafi haƙƙin Sarki Aminu Ado Bayero
  • Mai shari'a Liman Muhammed ne ya yanke wannan hukunci a karar da Aminu Babbba Ɗanagundi ya shigar a zaman yau Alhamis
  • Wannan na zuwa ne bayan babbar kotun jihar Kano ta bayar da umarnin a gaggauta kai takardar sammaci ga sarakunan Kano biyar da aka rusa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Babbar kotun tarayya mai zama a jihar Kano ta bayyana cewa tana da hurumin sauraron ƙarar Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Mai shari'a Liman Muhammed ne ya yanke wannan hutuncin a shari'ar sarautar Kano a zaman kotun na yau Alhamis, 13 ga watan Yuni, 2024.

Kara karanta wannan

Kotun koli ta tanadi hukunci a shari'ar da Tinubu yake yi da Gwamnoni 36

Aminu Bayero da Sanusi II.
Babbar kotun tarayya ta ce tana da hurumin sauraron ƙarar Aminu Bayero Hoto: @ImranMuhdz
Asali: Facebook

Sarkin Dawaki Babba, Aminu Baba Dan Agundi, shi ne ya shigar da ƙarar gaban ƙuliya kan tauye haƙƙin Sarki Aminu Ado, kamar yadda Channels tv ta rawaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shari'ar gwamnati da Sarki Aminu Ado Bayero

Lauyoyin Sarkin Kano na 15 sun ce an keta hakkin Mai martaba na zama ‘dan kasa wajen sauke shi daga kan karagar mulki.

Wadanda suka kare gwamnati sun fadawa babban kotun tarayyar cewa sarauta ba hakki ba ne, gata ce da aka yiwa basaraken.

Lauyan da ya tsayawa gwamnati ya ce lokacin da aka shigar da karar, Aminu Ado Bayero ya rasa rawaninsa na Sarkin Kano.

Kamar yadda aka ji, gwamnati da masarautar Kano ta bukaci a yi fatali da karar, inda ta ce babu dalilin sauraron Aminu Bayero.

Kotu za ta saurari shari'ar sarautar Kano

Babban kotun tarayyar ta ce tana da hurumin da za ta saurari korafin Aminu Ado Bayero a cewar rahoton da NTA News ta fitar.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: EFCC ta fadi dalilin kasa cafke tsohon gwamna kan badakalar N80bn

Wannan na zuwa ne bayan babban kotun jihar Kano ta umarci rundunar ƴan sanda ta kai takardar sammaci da Aminu Ado da sarakuna huɗu da aka tuɓe ma rawani.

Iyalan Nyass sun roƙi Sanusi II

A wani rahoton kuma Iyalan Sheikh Nyass sun bayyana matsayarsu kan rigimar sarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.

A wata sanarwa da Sheikh Muhammad Mahy Ibrahim Nyass ya fitar sun roƙi Sanusi II ya bi sahun kakansa, Muhammadu Sanusi I, ka da ya koma kujerar sarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262