Tsohon Shugaban Majalisa ya Fadi Babban Kalubalen Dimokuradiyya a Najeriya
- Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara ya gano babban abin da ke kawo cikas ga tsarin mulkin dimokuraɗiyya, musamman ta fuskar inganta rayuwar 'yan kasa
- A taron da ya gudana a Ikeja da ke Legas, Rt. Hon. Dogara ya bayyana talauci da ya yi wa 'yan kasa katutu a bangarori da dama da babban kalubalen tsarin mulkin dimokuradiyya
- Tsohon kakakin majalisar na ganin yawaitar talauci tsakanin 'yan kasar nan manuniya ce kan yadda dimokuraɗiyyar ta gaza cicciba rayuwar al'umma ko wadata su da abin da su ke bukata
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Yayin da Najeriya ke bikin cikarta shekaru 25 ana mulkin dimokuradiyya ba tare da juyin mulki ba, tsohon kakakin majalisar wakilar Yakuba Dogara ya bayyana babban kalubalen da tsarin mulkin farar hular ke fuskanta.
Yakubu Dogara ya gano cewa tsagwaron talauci ne babban matsalar da ke hana dimokuradiyya tafiya yadda ya kamata.
Daily Trust ta wallafa cewa tsohon shugaban ya fadi haka ne a wani taro da ya gudana a otal din Marriott da ke Ikeja a jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Dimokuradiyya ba ta taimakon 'yan kasa," Dogara
Tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya ce tsarin mulkin dimokuradiyya bai tsinanawa 'yan Najeriya komai. Ya fadi haka ne ta sanarwar da hadiminsa Turaki Hassan Adamu ya fitar yayin da kasar nan ke bikin cika shekara 25 ana mulkin dimokuradiyya, kamar yadda Business Day ta wallafa.
“Dimokuradiyyar mu ba ta aiki wajen inganta rayuwar da yawa daga 'yan kasar nan. Duk da su na raye kuma su na da 'yanci, amma ba sa iya samun wani farin ciki,"
- Yakubu Dogara
Tsohon Kakakin ya yi zargin rashin ingantattun tsare-tsaren gwamnati ne ke jefa 'yan kasa cikin kangin talauci, saboda haka ya bukaci a matsawa gwamnatin lamba domin ta dauki matakan inganta rayuwar 'yan Najeriya.
Yakubu Dogara ya sauya sheka
A baya mun kawo mu ku labarin cewa tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya sauya sheka daga jam'iyyarsa ta APC zuwa PDP. Ya dauki matakin ne bayan ganawa da kusoshin APC mabiya addinin kirista da dattawa a Arewa a fadan da su ke da tikitin musulmi da musulmi na shugaban kasa da mataimakinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng