Dangote Ya Sha da Kyar a Hannun ‘Ubannin Daba’, Ana So a Lalata Matatar Man da Ya Gina
- Attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya ce ya biya kusan $2.4bn daga cikin $5.5bn da ya karbo bashi domin gina matatar mansa
- Aliko Dangote ya bayyana cewa wasu ‘yan kungiyar ‘ubannin daba' na cikin gida da na waje sun yi kokarin lalata matatar man
- Dangote ya ce yana sane da cewa zai samu abokan hamayya, amma bai yi tsammanin adawar za ta yi tsauri har hakan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bahamas - Aliko Dangote ya bayyana cewa wasu ‘yan kungiyar ‘ubannin daba' na cikin gida da na waje sun yi kokarin lalata matatar man sa ta dala biliyan 19 da ya gina.
Dangote ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron shekara-shekara na bankin Afreximbank (AAN) a Nassau, Bahamas, ranar Laraba.
Ubannin daba na kai wa Dangote hari
Da yake jawabi a taron, Dangote ya ce ubannin daba a harkar mai sun fi karfin ubannin daba na harkar magunguna wajen dakile abokan hamayyarsu, in ji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar attajirin Afrikan, ubannin daba da dama sun yi iya bakin kokarinsu domin ganin sun lalata matatar da ke sarrafa ganga 650,000 a kowace rana.
Dangote ya ce yana sane da cewa dole ya samu abokan hamayya a duniyar mai, amma bai yi tsammanin adawar za ta yi tsauri haka ba.
Dangote ya fara biyan bashin $2.4bn
Jaridar The Cable ta ruwaito Dangote ya kuma ce ya biya kusan dala biliyan 2.4 daga cikin dala biliyan 5.5 da ya karbo bashi domin gina matatar mansa ta dala biliyan 19.
Dan kasuwar ya ce mutane da dama sun yi tunanin ba zai iya kammala aikin gina matatar ba, inda ya ce ba domin tallafin bankin Afreximbank da Access ba, da komai ya lalace masa.
“Mun aro kudin ne bisa ma’aunin abin da muke iya biya. Ina tsammanin mun aro akalla dala biliyan 5.5. Amma mun biya riba mai yawa saboda tsaikon da muka samu.
“Iya bashin da muka karba kenan, kuma zuwa yanzu mun biya $2.4bn. Mun yi kokari sosai, komai na tafiya yadda muka tsara, yanzu $2.7bn ake bin mu."
- Aliko Dangote
'Yan daba sun kai hari Katsina
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu gungun 'yan bindiga sun kai hari kauyukan karamar hukumar Kankara da ke jihar Katsina tare da kashe farar hula da jami'an tsaro.
An ce 'yan bindigar sun kuma kashe fararen hula 22, jami'an 'yan sanda hudu da kuma 'yan kungiyar tsaro ta KSCWC guda biyu a wannan harin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng